Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya ziyarci jihar Bauchi inda ya yi gaisuwa ga iyalan marigayi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi bisa rasuwar marigayin wanda ya rasu ranar Alhamis, 24-11-2025.
A ziyarar ta’aziyyar, Saraki ya samu tarɓa ta musamman daga malamai da shugabanni da al’ummar jihar Bauchi, waɗanda suka fito domin tararsa.
- Fita Daga PDP: Babu Wani Abu Da Zai Cutar Da PDP, Jam’iyyarmu Za Ta Ƙara Haɓaka – Bukola Saraki
- An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano
“Marigayi Sheikh Ɗahiru Bauchi ya kasance malamin da za a yi kewa musamman wajen faɗin gaskiya da yadda yake mu’amala ba tare da nuna bambanci ba”. A cewar Saraki
Ya ƙara da cewa “Na yi addu’ar Allah ya jiƙansa da rahama ya gafarta masa kurakuransa sannan ya bawa iyalansa da miliyoyin mabiya ɗariƙar Tijjaniyya da al’ummar musulmi baki ɗaya haƙurin jure rashinsa. Na kuma yi masa addu’ar Allah ya sanya shi a Aljanna Firdausi”.
Tun kafin zuwansa jihar Bauchi, Saraki ya fara miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin da al’ummar musulmi baki ɗaya a shafukansa na sada zumunta.














