Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Laraba, 27 ga watan Satumba, 2023 a matsayin ranar hutu domin gudanar da bukukuwan shekara na maulidin Annabi Muhammad (SAW).
Ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, wanda ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya, ya taya daukacin al’ummar Musulmi na gida da na kasashen waje murnar zagayowar bikin na bana.
- Nutsuwa Da Dattakun Annabi Muhammadu (SAW)
- Tausayi Da Kyawon Cika Alkawarin Annabi Muhammadu (SAW) II
Tunji-Ojo, a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakatare na ma’aikatar, Dakta Oluwatoyin Akinlade, a ranar Litinin din da ta gabata, ya gargadi ‘yan Nijeriya, musamman matasa da su kasance cikin ruhin soyayya, hakuri, da juriya don koyi da Annabi Muhammad (SAW) ), ya kara da cewa, yin hakan zai tabbatar da zaman lafiya, tsaro da hadin kai a tsakanin al’ummomi a kasar.
Ya kuma bukaci ‘yan Nijeriya da su rungumi dabi’ar aiki tukuru da neman zaman lafiya ga abokan zamansu, ba tare da la’akari da banbancin addini, akida, zamantakewa da kabilanci ba, sannan kuma su hada kai da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a kokarinta na samar da ci gaba da kasa wacce kowa ke kwadayi kuma duk ‘yan kasa za su yi alfahari da ita.
Ministan ya taya daukacin musulmi farin cikin yin bukukuwan Maulidin cikin kwanciyar hankali da budi da wadata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp