Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Barista Nyesome Wike, ya taya daukacin mazauna babban birnin tarayya murnar bikin Mauludi, inda ya bukace su da su bi tsarin zaman lafiya, tausayi da hadin kai a tsakaninsu.
A sakonsa na bikin Mauludi ga mazauna garin, Ministan ya bukaci al’ummar Musulmi da sauran mazauna babban birnin tarayya Abuja da su hada kai, su yi amfani da bikin a matsayin wata dama da za su sake jaddada aniyarsu ta juriya, soyayya da kyautatawa kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya koyar.
- Bukukuwan Maulid: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Laraba Ranar Hutu
- Gwamnatin Tarayya Zata Gina Manyan Tituna Na Zamani A Abuja-Lagos Da Fatakwal-Lagos
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ministan ya sanya wa hannu da kansa, wadda aka raba wa manema labarai a Abuja a ranar Talata, inda ta ce: “Abin farin ciki ne in mika gaisuwata ta musamman a madadin hukumar babban birnin tarayya Abuja ga daukacin mazauna Babban Birnin Kasar (FCT) akan taya murna da farin ciki ga zagayowar wannan gagarumin biki na Mauludi. Wannan rana mai muhimmanci ita ce ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW) kuma lokaci ne da muke bukatar koyarwarsa ta aminci da tausayi da hadin kai.
“Mauludi ba wai murnar bikin maulidin ne kawai ba; wata dama ce a gare mu da ya dace mu taru a matsayinmu na mazauna babban birnin tarayya Abuja domin tabbatar da aniyarmu ta bin dabi’un hakuri da kauna da kyautatawa kamar irin yadda Annabi Muhammad SAW ya yi ta wa’azantarwa ba tare da gajiya ba. Lokaci ne da ya kamata mu tuna da mahimmancin tausayawa da kyawawan halaye na hadin kai wadanda ya kamata su jagoranci mu’amalar mu da juna.
“Allah ya sa wannan bikin Mauludin ya kawo mana zaman lafiya da walwala da budi. Mu tuna da darussan da Annabi Muhammad ya wa’azantar da mu, mu yi kokarin koyi da kyawawan dabi’unsa a cikin rayuwarmu ta yau da kullum”. Inji ministan