Gwamnatin Tarayya ta sanya hannun yarjejeniyar fahimtar juna da Jamhuriyar Cuba, don bunkasa harkokin kere-kere, kimiyya da kuma fasaha a tsakanin kasashen biyu tare da kyautata harkokin ci gaba mai maidorewa.
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, shi ne ya jagoranci tawagar Nijeriya wajen sanya hannun yarjejeniyar a yayin taron ‘G77+China Summit’ da ya gudana a Habana, kamar yadda wata sanarwa wadda Daraktan Yada Labarai na ofishin Mataimakin Shugaban Kasar, Olusola Abiola ya fitar a karshen makon da ya gabata.
Ministan Kere-kere, Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji wanda ya sanya hannu a madadin Gwamnatin Nijeriya, ya jinjina wa salon mulkin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu, sakamakon kai wa ga cimma wannan yarjejeniya.
Hadakar yarjejeniyar, za ta mai da hankali a bangarorin bincike da ci gaban harkokin rayuwar jama’a da kuma kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu.
Bangarorin hadin guiwar tsakanin kasashen biyu, zai mai da hankali ne a kan fasahar kere-kere, binciken kimiyya, sabbin kirkire-kirkiren zamani, ci gaban fasaha, bunkasa harkokin rayuwar al’umma, musayar ra’ayoyin kwarewa kan kimiyya da kuma fasaha da kere-kere, domin musayar ra’ayoyi ta yadda za a samu bunkasar ci gaba mai muhimmancin gaske.
Nnaji ya kara da cewa, Kasar Nijeriya za ta bayar da cikakkiyar gudunmawar da ake bukata daga gare ta, domin cimma nasarorin da yarjejeniyar ta sanya a gaba, ya sake jaddada cewa, gwamnati a shirye take ta aiwatar da tsare-tsaren yarjejeniyar da aka cimma.
Daga cikin wadanda suka shaidi wannan kyakkyawar kafa ta tarihin ci gaban kasashen biyu, sun hada da Babban Sakataren Ma’aikatar kula da harkokin cikin gida, Ambasada Adamu Lamuwa, Ambasadan Nijeriya a Kasar Cuba, Ambasada Ben Okoyen tare da sauran manyan jami’an gwamnati.