Sannu a hankali, kasar Sin da Nahiyar Afirka na kara gina ‘yan uwantaka da yaukaka zumunci mai dadi a tsakaninsu bisa kawancen kasuwanci da bunkasa hada-hadar tattalin arziki domin cin gajiyar juna.
Aniyar kasar Sin ta ganin kasashen Afirka sun tsaya da kafafunsu da kuma amannar da suka yi cewa tabbas kawancensu da Sin ba karamin alheri ba ne, sun haifar da da mai ido bisa yadda Sin ta zama babbar kawar Afirka ta kasuwanci da babu kamarta a cikin shekaru 15 a jere, kana ta hudu wajen zuba jari a nahiyar.
Harkokin kasuwanci da zuba jari ba su samun tagomashi matukar babu ababen more rayuwa. Shi ya sa shawarar “Ziri Daya da Hanya Daya” wanda Sin ta kulla kawance a karkashinta da kasashen Afirka 52 da ma kungiyar tarayyar Afirka (a karshen 2022), ta kasance alfijir ga samar da dimbin ababen more rayuwa domin hanzarta kawo ci gaban da ya kamata a Afirka.
Yanzu haka, kamfanonin Sin fiye da 3,000 da ke aiki a nahiyar, suna gudanar da ayyukan kawo ci gaba daban-daban har ma an sami nasarar gina ko gyara layin dogo fiye da kilomita dubu 10 da titinan mota su ma kimanin dubu 100, baya ga tasoshin jiragen ruwa kusan 100.
Sakamakon burin da Sin take da shi na cin moriyar juna a tsakaninta da Afirka, alkaluman baya-bayan nan sun nuna cewa a shekarar 2023, kasuwancin da ke tsakanin Sin da Afirka a mizanin shekara-shekara, ya habaka zuwa dala biliyan 282.1. Inda bangaren motoci masu aiki da sabbin makamashi ya karu da kashi 291 bisa dari sai baturan ‘lithium’ da Sin ke fitarwa zuwa nahiyar da ya karu zuwa kashi 109. Kana a hannu guda kuma, kayayyakin da Sin ke sayowa daga Afirka na amfanin gona masu kwaya suka karu da kashi 130 yayin da na kayan lambu suka habaka da kashi 32.
Abin bai tsaya nan ba, domin ganin Afirka ta kara samun damar kai kayayyakinta zuwa kasuwannin kasar Sin, kasar ta yi rangwamen biyan haraji da kashi 98 cikin dari a kan kayayyakin da ake biya musu harajin kwastam daga kasashe 20 da suka fi fuskantar koma-baya a nahiyar.
Bugu da kari, a farkon watanni shida na wannan shekarar kawai, kayayyakin da Sin ke shigowa da su kasarta daga Afirka sun kai na kimanin dala biliyan 60.1 wanda yake nuna an samu kari da kashi 14 a mizanin shekara-shekara. Haka nan, bayanai sun nuna cewa amfanin gonar da Sin ke shigo da su kasarta daga Afirka yana kara habaka inda a bana aka cika shekara bakwai a jere abin yana samun tagomashi.
Har ila yau, jarin da Sin ke zubawa a Afirka zuwa karshen 2023 ya zarce dala biliyan 40. A sakamakon haka ne ma, mu a nan Nijeriya muka samu tashar teku mai zurfi a Lekki da ke Jihar Legas wadda tuni manyan jiragen ruwa suka fara hada-hada a ciki. A baya, babban jirgin da zai zo tsohuwar tashar jiragen ruwa na Legas shi ne mai daukar kwantena 6,000 amma bisa samar da sabuwar tashar Lekki da taimakon kasar Sin, tuni har wani jirgin ruwa na kasar Faransa mai daukar kwantena 15,000 ya zo tashar don sauke kaya, inda hakan ke nuna cewa Nijeriya ta samu gagarumin ci gaban hada-hadar jiragen ruwa.
A birnin Accra na kasar Ghana kuma, bisa taimakon kasar Sin, an zamanantar da tashar jiragen ruwan kamun kifi na zamani a Yankin Jamestown, da gyara tsohuwar tashar jiragen ruwa ta Bata a kasar Equatorial Guinea, sannan a 2023 kuma, an aza harsashin gina tashar jiragen ruwa na kamun kifi ta Kilwa a kasar Tanzania.
Akwai misalai da daman gaske da ke alamta yadda gaba za ta yi kyau a tsakanin Sin da Afirka bisa yadda harkokin cinikayya da tattalin arziki ke kara samun tagomashi.