Shekarun nan na baya, wasu kafofin yada labarai na yamma sun yi ta karawa batun yawan jama’ar kasar Sin gishiri, musamman ma bayan da asusun kula da yawan jama’a na MDD ya gabatar da rahoton yanayin yawan jama’ar duniya na shekarar 2023 a ran 19 ga watan nan, inda aka yi kiyasin cewa, zuwa tsakiyar bana, yawan jama’ar kasar Indiya zai zarce Sin, inda Indiya za ta kai matsayin farko a duniya a bangare yawan jama’a, suna masu cewa, yanzu Sin za ta rasa fifikonta a fannin yawan jama’a, abin da zai haifar da koma bayan tattalin arzikinta.
To, shin ko wadannan kafofin yada labarai sun fadi gaskiyar halin da ake ciki a wannan fanni a Sin? Bari mu kalli alkaluman da aka fitar.
Ko da yake Sin na fuskantar wasu sabbin sauye-sauye a fannin yawan jama’a, amma har yanzu tana da ma’aikatan kwadago masu dimbin yawa. Sin ta gudanar kidayar jama’a a karo na 7 a shekarar 2020, alkaluma na nuna cewa, yawan al’umma masu shekaru tsakanin 16 zuwa 59 ya kai miliyan 880, kuma matsakaicin shekarunsu da haihuwa ya kai 38.8, wannan adadi ya nuna cewa, yawan masu jini a jika a kasar ya kai fiye da kashi 60%, wadanda suke taka muhimmyar rawa wajen ayyukan raya kasar. Kazalika, yawan yara na karuwa. Alkaluma na nuna cewa, yawan al’ummar kasar masu shekaru tsakanin 0 zuwa 14 ya karu da kashi 1.35% a cikin shekaru 10 da suka gabata, wanda ya kai kashi 17.95% na dukkan al’ummar kasar, wanda hakan ke zama tushen karuwar ma’aikatan kwadago a kasar a nan gaba.
A wani hannu na daban, fifikon yawan jama’a ba a fannin yawansu kadai yake bayyana ba, har ma da fannin kwarewarsu. Mai lambar yabo ta Nobel a fannin tattalin arziki Thodore W.Schults, ya dade yana nazari kan batun alakar tattalin arziki da ingancin jama’a, a ganinsa kwarewar jama’a na iya ingiza bunkasuwar tattalin arziki, don haka dole ne a inganta kwarewar jama’a. Alal misali, idan ana son yin girbi mai armashi, ba ma kawai ana bukatar gonaki masu fadi ba, kamata ya yi a shirya irrai masu inganci da amfani da taki mai kyau da sauransu.
Sin tana yin iyakacin kokarin bunkasa sha’anin ba da ilmi, matakin da ya sa matsakaicin matsayin samun ilmi na jama’ar kasar ya karu matuka. Ya zuwa yanzu, yawan mutanen kasar da shekarunsu ya kai shiga makarantar sakandare da jami’a wadanda kuma suka sama damar ya kai kashi 91.4% da 57.8%, adadan da suka karu da kashi 6.4% da 27.8% bisa na makamancin lokaci na shekaru 10 da suka gabata.
Bisa kididdigar da ma’aikatar ba da ilmi ta kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2021, matsakaicin shekarun da ma’aikatan kwadago suka kwashe wajen samun ilmi ya kai shekaru 10.9, wanda ya karu da shekara 1 bisa na shekarar 2012, a yayin da wannan adadi ya kai shekaru 14 ga karin sabbin ma’aikatan kwadago da aka samu a shekarar 2022, abin da ya nuna cewa, kwarewar ma’aikatan kwadago ya samu karuwa matuka. Wadannan adadai na samun karuwa a ko wace shekara, matakin da ya nuna cewa, kwarewar jama’ar kasar na ci gaba da karuwa, tare da samar da tallafi ga bunkasuwar tattalin arziki da al’ummar kasar Sin mai inganci.
Yawan jama’ar kasar Sin na rika karuwa, kuma kwarewarsu na dada ingantuwa, wadanda suke samun ilmi na zamani, zaman rayuwar jama’a na rika samun kyautatuwa, Abin da ya nuna cewa, fifikon da Sin take da shi a fannin yawan jama’a bai bace ba, ya zama sabon iri wato ingantuwar kwarewar jama’a. (Mai rubuta da fassarawa: MINA)1