Hausawa na cewa ‘Da Rarrafe Yaro Kan Tashi’, haka ya ke ga masu maida hankali kan al’amuran da suka sa a gaba dan cinma burinsu. Bakon mu na yau JAMILU ISAH (JEY BOY) Matashin Mawaki ne wanda wakokinsa ke zagawa a yanzu, ya bayyanawa masu karatu dalilinsa na fara waka, tare da irin nasarorin daya samu a fannin waka, ya kuma yi kira ga masu kokarin shiga harkar waka tare da bayyana irin kalubalen daya fuskanta wajen mutane kafin ya fara wakkr, har ma da wasu batutuwan masu yawa. Ga dai tattaunawar tare da LUBABATU AUTA INGAWA:
Da farko masu karatu za su so su ji cikakken sunanka tare da dan takaitaccen tarihinka…
Sunana Jamilu Isah Abubakar, amma an fi sanina da Jey Bouy. An haife ni a unguwar Bridget Gama a sheka ta 2000.
Me ya ja hankalinka har ka tsunduma harkar waka, kuma da wacce waka ka fara?
Abin da ya ja hankalina na fara waka, gaskiya ni mutun ne me san ba da shawarwari, kuma harkar waka tana da hanyoyin isar da sako ga al’umma. Wakar da na fara na yi a kan irin samari su tashi su nemi kudi, saboda rayuwa gaskiya sai an tashi an nema. Kuma ‘time’ din da nayi wannan waka nayi ta ‘around 2018’ sunan wakar ‘Money’.
Ko akwai wani kalubale da ka fuskanta wajen iyaye, musamman lokacin da ka je musu da maganar kana son fara waka?
Gaskiya da yake mahaifin mu mutun ne me fahimta ya dade yana aiki a America a bisa haka gaskiya al’adar su ta zama kusan daya, saboda yadda yayi da su in kazo da abu Kano so in ya duba ya gani kuma abin nan zai iya zama hanyar cin abincinka kawai zai yi maka wa’azi ne ya ce ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma Allah ya sa ya zama hanyar cin abinci. Haka kuma ta wajan uwa mahaifiyar ta malamar asibiti ce ita gaskiya ‘same to my father’ sannan kuma kafin a zo inda ake daman yayata na fim Maryam Isah Abubakar wacce aka fi sani da Maryam Ceeter, sannan akwai mawakiya Aisha Isah Abubakar wacca aka fi sani da Aisha Gama, kuma abin ka ga family mu ba wanda ya ji yana son shiga ‘Industry’ ta dalilin wani, kowa da akwai abin da ya ja hankalinsa.
To! ya batun ‘yan uwa da abokanan da mutanen unguwa fa, ko akwai wani kalubale da ka fuskanta daga gare su?
Gaskiya akwai kalubale ta wajen abokanai na, wasu suna cewa ba zai yi maka kyau ba, waka ba naka bane, kawai ka mayar da hankali wajan karatu kawai. Sannan kuma wasu suna yin addu’a Allah ya sa haka shi ya fi alkairi, wasu kuma murna suke maza da mata.
Mu dan koma baya kadan, ka ce Maryam Isah yayarka ce, mece ce alakarka da Mansura Isah?
Eh! Mansura Isah ‘Cousin Sister’ na ce.
Daga lokacin da ka fara waka kawo iyanzu kayi wakoki sun kai kamar guda nawa?
Guda 15, amma akwai guda uku da zan saki a kwanakin nan, sannan kuma a cin 15 ba kowace take kan yanar gizo ba.
A gaba daya wakokin da kayi wacce ce bakandamiyarka, kuma akan me kayi wakar?
Gaskiya na fi son ‘Jey Bouy ta iya rawa’, saboda Anty Maryam tana son wakar. Na yi wakar akan nishadin mu na hausawa.
Misali wani ya zo wajenka kan yana son ka bashi shawara game da yadda zai fara waka, wacce shawara za ka bashi?
Gaskiya shawara ta farko ita ce ya fara zuwa ya gama da magabata.
Wanne irin nasarori ka samu game da waka?
Na samu nasarori da yawa ciki akwai masu kira na akan wakokina, suna fadan sakon da na bayar ya isa gare su, sannan kuma akwai ‘bideo’ da nayi aikinsu wajan guda biyar wanda da a baya ba ni da ‘bideo’ ko daya watan da zamu shiga zan saki guda biyu.
Idan na fahimce kana ka, son fidda album kenan?
Eh! in sha Allahu, muna kan aikin album din a yanzu haka, in sha Allah yana nan fitowa.
Wanne kira za kai ga masu kokarin fara waka?
Kiran da zan yi gare su shi ne, su maida hankaki kan abin da suka sa a gaba, sannan su zamo masu yawaita nazari da buncike dan kyautata wakarsu.
Wanne kira za ka yi ga sauran mawaka ‘yan uwanka?
Shawara ta da masu tasowa shi ne su dinga daukar shawarar manyansu wajan ‘recording’.
Me za ka ce ga makaranta shafin Rumbun Nishadi?
Su ci gaba da bibiyar shafin, domin jin gaskiyar bayanai daga bakin bakin da aka gayyato.
Me za ka ce da ita kanta Jaridar LEADERSHIP?
Allah ya kara d’aukakata a fadin duniya gaba daya, Allah ya saka musu da alkhairi.