A wannan makon mun klawo muku ci gaba hirar da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi da daya daga cikin fitattun Jaruman, wanda ya shafe shekaru ashirin da biyar a cikin masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, ALI IBRAHIM wanda aka fi sani da ALI DAWAYYA. A wanann makon hirar ta tabo bangarori da dama na rayuwarsa a masana’antar fim da irin burinsa a nan gaba. Ga dai yadda hirar ta kasance.
A fina-finan da ka fito ciki, wanne ne ya zamo bakandamiyyarka?
Bakance da Raga da ‘Ya daga Allah da Sai Naga Ali da Daga Ni Sai Ke, Bakauye, sai Manyan Mata siris da Izzar So siris da Binta Suga siris da Wata Daya siris, ga Barauniyar Amarya siris da Daukaka siris, da Bana Bakwai na FKD.
Ko akwai wani fim da ka taba yi wanda ka yi da ka sanin yinsa?
Gaskiya babu.
Wanne fim ne wanda ka yi ka sha wahalar yinsa, kuma wanne ne ya baka dariya, wanne ne ya baka takaici lokacin da ka ke yin fim din?
Manyan Mata siris da Binta Suga siris, sun bani wahala sosai, akwai Sai Naga Ali da Bakauye.
Me ya baka wahala a cikin fim din?
Ni ne furodusa kuma ni ne Akto.
Wanne irin nasarori ka samu game da fim?
Na samu Nasarori sosai na yi aure, ina da ‘ya’ya uku saura biyu daya ta rasu.
Me ka ke son cimma game da fim?
Na zama ‘International Actor’ a duniya, kuma na kawo ci gaba a masana’antar Kannywood yadda kowa zai tsaya da kafar shi da izinin Allah.
Bayan sana’ar fim shin kana wata sana’ar ne?
Eh! ni dan kasuwa ne kuma dan kwangila.
Wanne abu ne ya fi damunka idan ka ji ana fadawa ‘yan fim?
Mutum ya yanke ma hukunci bai sanka ba ko a yi muku kudin goro.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ka taba iya mantawa da shi a rayuwa ba?
Da-na tsinci kaina a musulmi kuma masoyin Allah da manzon Allah, na rashin jin dadi kuma shi ne da-na tafi gidan yari ba da hakkina ba.
Kafin ka fara fim wanne jarumi ko jaruma ce ta fi birge ka cikin masana’antar Kannywood kuma me ya sa?
Mutum uku ne Ali Nuhu da Ahmad S. Nuhu da Gagare wanda ya yi fim din ‘Sunbuka’ na kamfanin Sarauniya, Mace kuma Hauwa Ali Dodo da Fati Mohammed. Saboda suna da mu’amula da kuma tarbiyya.
Ka taba yin fim da Gagare?
A’a ba mu taba haduwa ba ya riga ni fara fim.
Su wa ka fi so su fito matsayin iyayenka a fim, kuma me ya sa?
Hajara Usman da Usaini Sule Koki da Ibrahim Mandawari, ina so ne saboda dacewar su duk dan kallon da ka ce su ne iyayenka an san babu yarinta a ‘cast’ din fim din shi ne ya sa nake sansu.
Wane ne babban abokinka a cikin masana’antar Kannywood?
Babban abokina Haruna Talle Mai Fata.
Da wanne jarumi ko jaruma ka fi son yin fim da shi?
Ali Nuhu da Adam A Zango, mata kuma ba ni da zabi gaskiya.
Mene ne burinka na gaba game da fim?
Na kawo ci gaban da ba a taba tunani ba da izinin Allah.
Ya alakarka take da sauran abokan sana’arka?
Muna zaune lafiya, muna ganin darajar juna.
Wanne irin kalubale ka fi fuskanta wajen gudanar da ayyukanka, kuma ta wacce hanya ka ke ganin za a shawo kan matsalar?
Kalubalen da na samu shi ne; Dana rike iya fim shi ne sana’ata, saboda duk wanda ya rike iya fim shi ne sana’arshi ba shi da sana’a, dole ka zama dan kasuwa. Duk sana’ar da ba za ta kawo maka 500 ko 1000 kullin ba, ba sana’a ba ce. Ya kamata duk wani dan fim ya zama yana da ‘plan’, ko wajan cajin waya ne ka tsira da shi, shi ne gaskiyar magana, dan har kana so ka zauna da iyalanka lafiya da kuma iyayenka da abokanka da ‘yan uwa ba za ka dame su da roko ba.
Za mu ci gaba.