Babban daraktan sashen lura da kan iyakoki, noman rani da kiyaye yankunan tarihi, a ma’aikatar kula da muhalli, noma da kiwo na kasar Burundi Mr. Diomede Ndayirukiye, ya jinjinawa tallafin da kasar Sin ke baiwa kasar sa a fannin raya noma, matakin da ya ce ya yi matukar taimakawa kasar wajen samar da isasshen abinci.
Yayin zantawar sa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a baya bayan nan, Ndayirukiye ya ce a wannan gaba da kasar Sin ke cika shekaru 10 da kaddamar da shawarar “Ziri daya da Hanya Daya”, Burundi ta kasance cikin jerin kasashen da suka ci gajiya mai tarin yawa daga shawarar, don haka mahukuntan kasar ke godewa Sin kan hakan.
Jami’in ya kara da cewa, yayin wa’adin aikin tawaga ta 5, ta kwararrun Sin a fannin raya aikin noma a Burundi wanda ya kammala a kwanan nan, kasar ta cimma manyan nasarori, musamman a fannin tagwaita irin shinkafa.
Ya ce, “Mun daga matsayin yabanyar da ake samu, daga tan 3 zuwa 4 na shinkafa zuwa tan 10 ko ma 11 a duk hekta, sakamakon fasahohin kwararrun na kasar Sin. Kaza lika a yanzu, a kalla lardunan kasar 13 cikin 18 suna noma nau’o’in shinkafa daban daban cikin nasara.
Ndayirukiye, ya ce bisa fasahohin zamani na noman kifi da kaji irin na Sin, manoman Burundi sun samu karin nasarori, suna kuma godiya ga tallafin bangaren Sin a wannan fage. (Saminu Alhassan)