A halin da ake ciki a yanzu a bangaren masu yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu suna kallo Shugaban kasa Muhammadu Buhari kamar irin tsohon aboki da aka bata da shi a baya, wanda wannan zamantakewar ta yi tsami a tsakanin bangarorin biyu.
Magoya bayan Tinubu da gwamnonin jam’iyyar APC suna sukan dokar Buhari na sauya naira a matsayin abun da bai dace ba, kuma ya saka talakawa cikin wahala.
- Me Ya Sa Amurka Ta Ga Balan-balan A Samaniya A Tsayin Mita 18000 A Maimakon Gajimare Mai Guba A Samaniyar Ohio Dake Kasar?
- Kasar Sin Za Ta Soke Haraji Kan Kayan Da Ake Shigowa Daga Habasha Da Burundi Da Nijar
Shi ma kansa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya zargi mutane da dama da suke yin masa bi-ta da kulli kuma suna nuna cewa kamar ba su suke yi ba. Ba don batanci ga wani ba, ina fatan Tinubu yana sane da cewa a yanzu yana tare da mutumin nan da ya rubuta littafin hatsarin ma’aikacin gwamnati wanda ya ware wasu shafuka har 4 a cikin littafin yana bayar da labarin yadda Atiku ya hana shi zambantar gwamnatin Nijeriya.
Ba wani lokaci mai tsawo ba, gwamnonin Arewa da Tinubu sun yi kira ga mutane da su goyi bayan gwamnati a kan duk wani abu da suke yi. A cewarsu, hakan shi ne kishin kasa. Amma a yanzu gwamnonin sai su tafi kafafen yada labarai suna bude wa Buhari wuta don ya warware masu matsalarsu a nan take, wanda zai kasance don biyan bukatarsu ne akarin kansu. Suna bukatar ya kara lokacin karbar tsofaffin kudade har sai bayan zaben shugaban kasa, don su cika alkawarinsu na ganin an zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa.
Kudurin Buhari na sauya naira shi ne ya kawar da sayen kuru’u. Ba kamar Buhari ba, shi Tinubu yana ganin wannan tsarin na sauya naira ana yin masa bi-ta da kullin zama shugaban kasa ne. Wasu jam’iyyun siyasa sun goyi bayan wannan kuduri, saboda suna ganin zai taimaka masu wajen daina amfani da kudi a lokutan zabe. Ina nan a kan ra’ayina na illar sauya kudi da amfani da dokar takaita yawon kudade da lokacin da aka bayar, wanda ba shi ne abun da za mu tattauan a yanzu ba. Haka kuma idan wannan tsarin doka da aka sanya an sami nasara, Nijeriya za ta zama kasa ta farko a duniya da ta yi amfani da sauya kudi don yaki da magudin zabe. A saboda haka, abu ne da ‘yan kasa suke bukata a gudanar da ingantaccen zabe kuma sahihi a Nijeriya wanda zai kara karfin tsarin dimokuradiyya.
Abubuwan da al’umma suke bukata shi ne, ya kamata su kasance a gaba a yakin neman zabe lokacin zabe ba wai son kai ba. A wannan karon, gwamnonin Arewa sun fi mayar da hankali ne a kan son ransu da biyan bukatar kansu. Za mu iya gane haka daga yanayin Ganduje da El-Rufai a lokacin da gwamnonin Arewa suka yi taro da Buhari. Wadannan mutanen guda biyu sun bar wasu tarihi a jihohin Arewa.
Ganduje ya yi korafin cewa wannan tsarin da Emefiele ya yi ne don cutar da wasu; ma’ana akwai manufa. Wanda ya rika kokarin kawo wasu bayanai da ke nuna wasu daga cikin gwamnati ba sa goyoin bayan Tinubu da har ya kai ga kunnin Buhari. Amma dai su al’umma suna gani.
A cewar Emefiele, manufarsa na sauya naira shi ne a aiwatar da dokar nan na rage yawon kudade a hannun jama’a wanda zai rage hauhawar farashin kayayyaki. Wannan abu ne mai kyau da za a iya nasara a kai duk da yake ba shi a littafan nazarin tattalin arziki. Dole mu yi amfani da kalamansa.
A fili dai Buhari ya nuna goyon bayansa ga Tinubu, har yana yakin neman zabe tare da shi ma ya kaddamar da shi a jiharsa ta Katsina da wasu jihohin. Gwamnoni sun san cewa Buhari dattijo ne kuma mai magana daya. Ya bayyana cewa shi ya tuntubi Emefiele. Wasu za su iya tuna abun da ya yi a shekarar 1984, kuma yana sane da irin kuncin rayuwar da mutane suka shiga a wancan lokaci.
Mazari kaka dan shekara 63 wanda ya fito kafafen yada labarai a mabambantan lokuta yana sukar abun wanda ba ya bin dokar kotu ma. A daidai lokacin ne da yake zantawa da BBC Hausa inda ya barje guminsa. Ya caccaki dattawan Arewa da wasu ‘yan Billa da kowa ke magana a kai. Ban so in yi magana a kan ra’ayinsa na dattawa al’umma za su yi masa alkalanci. Ya bayyana cewa shi fa ba ya tsoron kowa kuma bai taba tsugunawa kowa daga cikinsu ba. Sai ga wasu hotuna an zakulo ya tsuguna wa wasu daga cikinsu har da Aisha da yake fada da ita. Shin wadannan ‘yan Billa suna da karfi haka?
Akwai lokacin da ya taba zagin manya-manyan Nijeriya da suka bayar da gudunmuwa wajen gina kasa, wato Ahmadu Bello Sardauna da Azikiwe da Awolowo, kawai sun tara kudi ne abun su wanda suka amfana da shi a siyasance. Kuma ya ki neman gafara a kan wadannan kalamai nasa. A saboda haka, mene ne ba zai fada a yanzu ba? Batun gaskiya amsar ba zai yi dadi ba kuma sakamakon wadannan karyayyaki ba za su yi dadi ba.
A kasar da take da manyan matsaloli da yunwa sakamakon talauci da matsalar rashin kudi da karancin mai. Tinubu da kowa ya sanshi da sakin layi idan yana jawabi wanda kuma yake ta yawan maimaita wannan sakin layin, jagororin Yarbawa sun karbe shi. Wani daga cikin dattawansu ma yana kiran yaki idan mulkin shugaban kasa bai koma yankin kudu ba. Idan muka ci gaba da jin abubuwa irin haka da kuma maganganu daga bakin gwamnoni, tsarin dimokuradiyyarmu zai iya fuskantar barazanar.
A wani bangaren kuma, za su iya amfani da wata hanyar don ganin sun sauya wa shugaban kasa ra’ayi. Zai iya kasancewa ba daidai yake ba, amma kurakurai biyu ba za su taba zama gyara ba. A saboda haka, dimokuradiyyarmu da hukumominmu su ne abun da gwamnati ya kamata ta duba su, duban da ya dace.
Idan ba a dauki matakan da suka dace ba, Nijeriya na iya fuskantanr matsalar da ta faru a ranar 6 ga watan Janairu a zaben Amurka. Wannan zanga-zangar da Amurkawa suka yi ne, ‘yan Brazil suka kwaikwaya makonni kadan kafin zabe. Ga wadanda ba su sani ba, wannan rikicin ne ya zama matsala ga zaben kasar wanda ya yi kama da na Nijeriya. Idan haka ta faru, abun Allah ya kiyaye, hukumomi su tuna da wadanda suka haddasa.