Babban bankin Nijeriya (CBN) da hukumar kula da kadarorin Nijeriya (AMCON) sun sanar a hukumance cewa sun kammala yarjejeniyar sayar da hannun jarin (SPA) bankin Polaris ta hanyar Kamfanin Strategic Capital Investment Limited ( ‘SCIL’).
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da majalisar wakilai a ranar Larabar da ta gabata ta amince da siyar da bankin Polaris, tare da lura da cewa sayarwar an bi ka’ida da kuma amincewar shugaban kasa.
Wata sanarwa da daraktan sashen sadarwar kamfanoni na babban bankin CBN, Osita Nwanisobi, ya fitar a madadin CBN da AMCON, ta bayyana cewa Kamfanin SCIL ya biya kudin nagani ina so har Naira biliyan 50 domin mallakar hannun jarin bankin polaris kashi 100.
SCIL ya amince zai cika Sharudan yarjejeniyar mallakar hannun jarin, wanda zai biya kudi har Naira tiriliyan 1.305.
Da yake magana kan cinikin a ranar Laraba, 19 ga Oktoba, 2022, shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar wakilai da ke binciken siyar da bankin Polaris, Hon. Henry Nwawuba, ya ce ‘yan majalisar a lokacin da suke binciken wasu takardu da tsare-tsare masu yawa kan yadda aka siyar da bankin, sun gano cewa akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa an bi tsarin da ya dace wajen mallakar sayar da Bankin.