Dokar takaita cire tsabar kudi ta na’urar ATM da Babban bankin CBN ya gindaya, ta fara aiki a fadin Nijeriya a yau Litinin.
Bayan korafe-korafe da kiraye-kiraye da mutane da kungiyoyi suka gudanar, CBN ya ce a yanzu daidaikun mutane za su iya cire tsabar kudi har naira 500,000 yayin da kamfanoni kuma za su iya cire naira miliyan biyar duk mako.
Idan mutum na son cire kudin da ya fi wannan adadin da aka fitar, to za a caji kashi biyar cikin 100 ga daidaikun mutane, kashi 10 cikin 100 ga kamfanoni na yawan kudin da za a cire.
Babban bankin kuma ya umarci bankuna da su daina sanya tsoffin takardun kudi da aka sauya wa fasali a nau’rorin ATM.