Babban Bankin Nijeriya CBN ya sanar da tsararan hukuncin da zai dauka a kan bankunan hada-hadar kudade wato DBN da aka samu suna karkatar da kudade.
CBN ya bayyan haka ne, saboda kokarin da yake ci gaba yin a tabbatar da ana tura kudaden na isa zuwa inda aka tura su.
- Kotu Ta Hana CBN Da Sauransu Yi Wa Kudaden Kananan Hukumomi Katsa-Landan
- Man Fetur Da Ake Shigowa Ya Ragu Da Kashi 35 – CBN
Bankin ya bayyana haka ne, a cikin sanarwar da ya fitar mai dauke da kwanan wata 13 ga watan Nuwambar 2024.
CBN ya yi gargadin cewa, duk bankunan da aka samu da karkatar da kudaden, za a kakama masa tarar da ta kai kashi goma daidai da jimlar kudaden d aka cire daga cikin kudaden.
Mukaddashin Daraktan riko a sashen gudanarwa na CBN Muhammad Olayemi ya jaddada cewa, matakan za su taimaka wajen cin zarafin takardar Naira da kuma tabbatar da kudaden da aka tura, sun isa ida aka bukata.
Kazalika, sanarwar ta kuma bayyana cewa, akawai bukatar bankuna su ci gaba da tabbatar da masu ajiya a bankuna suna yin amfani da na’urar ATM, musamman domin a kara karfafa wa jama’a gwiwa da maimakon yin dogaro a kn hanyoyin da ba a amince da su a hukuman ce ba.
Bankin na CBN, ya bayar da wannan umarnin ne, biyo bayan yadda ake yawan samun sabbin takardun Naira a kasuwanni, wanda hakan ke sanya wasu ke sayar da su.
Duba da yadda aka saba samun bukatar sabbin takardun kudade a lokacin gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara,ana kuma kara samun yawan yawon sabbin takardun kudade a kasanan, wanda hakan ya sanya CBN ya kara dauka tsaurara daukar matakai, musamman domin mutane su rinka cire kudade a hanyar ATM.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp