Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana cewa ritayar da ma’aikatansa 1,000 za su yi kwanan nan ba tilasta musu aka yi ba.
Ya ce ma’aikatan ne suka yanke shawarar barin aiki da kansu.
- Gwamna Sule Ya Rushe Majalisar Zartarwar Nasarawa, Ya Sauke Sakataren Gwamnati
- An Yi Taron Ƙungiyar Baburawa Na Abuja Cikin Annashuwa
Wannan bayanin ya fito ne yayin zaman sauraron bincike da Majalisar Wakilai ta gudanar kan ritayar da kuma shirin biyan ma’aikatan Naira biliyan 50.
Da yake jawabi ta bakin Daraktan Sashen Ayyuka na CBN, Bala Bello, ya ce ritayar ma’aikatan na cikin shirin sauya fasalin ayyuka don inganta aikin bankin da magance matsalar cunkoson ma’aikata.
Ya jaddada cewa babu wanda aka tilasta masa barin aiki, domin shirin yin ritaya daga aiki bisa raɗin kai ne daga ma’aikatan.
Shugaban kwamitin binciken, Hon. Usman Bello Kumo, ya tabbatar da cewa binciken cikin adalci, tare da duba sahihanci da manufofin shirin, da kuma tabbatar da cewa an gudanar da komai cikin gaskiya.