Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya kara yawan kudin ruwa da ake bai wa masu rance a bankunan da maki 200 wanda ya tashi daga kaso 22.75 zuwa kaso 24.75.
Sai dai masana tattalin arziki sun bayyana cewa za a iya amincewa da matakin idan na gajeren zango ne.
- Karancin Abinci: Gwamnatin Tarayya Za Ta Kafa Sansanin Soji A Tafkin Chadi
- Sojoji Sun Wanke Fursunoni 200 Da Ake Zargin Alaka Da Boko Haram A Borno
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya yi bayani a kan matakai biyar da kwamitin manufofin kudi na bankin suka cimma a taronsu na wannan karon wadanda suka hada da kara yawan kudin ruwa da 200 zuwa 24.75 daga 22.75.
Sai kuma rike adadin ajiyar kudi na bankunan kasuwanci kan kaso 45 cikin 100 da dai sauransu.
Daraktan sashen manufofin kudin na CBN kuma sakataren kwamitin, Dakta Muhammad Musa Tumala, ya yi karin bayani a kan matakan da CBN ya dauka.
Ya ce kara kudin ruwa wani mataki ne na gajeren lokaci da zarar abubuwa sun daidaita za a koma yadda ake a da.
A wani bangare kuwa masanin tattalin arziki, Mallam Kasim Garba Kurfi, ya bayyana cewa matakin bankin CBN bai zo da mamaki ba saboda halin da Najeriya ta sami kan ta.
Idan ana iya tunawa a wani mataki na daidaita farashin dala, CBN ya fito da wasu tsare-tsare musamman da suka shafi ‘yan kasuwar canji, wanda bankin ya koma ba su dala da kansa.