ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, November 17, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

CBN Ya Kara Yawan Kudin Ruwa Zuwa Kaso 18 Cikin 100 Daga Kaso 17

by Sadiq
3 years ago
CBN

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya bayyana cewa, kwamitin manufofin kudin bankin ya kada kuri’ar kara yawan kudin ruwa da kashi 50 zuwa kashi 18 cikin 100 daga kaso 17 da digo 5 cikin 100.

Wannan mataki dai an dauke shi ne don dakile hauhawar farashin kayayyaki a halin yanzu da ya kai kaso 21 cikin dari kuma saboda a saukaka wa ‘yan kasa da kuma bunkasa tattalin arzikin kasar nan.

  • APC Da Uba Sani Ba Su Lashe Zaben Gwamnan Kaduna Ba -PDP
  • Sin Ta Yi Kira Da A Gaggauta Dawo Da Taimakon Kudin Da Ake Baiwa Sudan Ba Tare Da Wani Sharadi Ba

Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana matsayar da kwamitin da manufofin bankin ya cimma bayan taronsu na yini biyu wanda mambobi 10 suka amince da daga kudin ruwan daga kaso 17.5 cikin 100 zuwa kaso 18 wanda ke nufin an samu karin kashi 50 a kan yadda yake a da a ranar Talata yayin da yake karanta sanarwar taron MPC karo na biyu na 2023 a birnin tarayya Abuja.

ADVERTISEMENT

Malam Haruna Bala Mustapha, ne daraktan lura da harkokin bankuna na babban bankin CBN, ya ce taron kwamitin manufofin kudi da aka kammala a ranar Talata ya duba muhimman abubuwa ciki da matsalar hauhawar farashi da ya addabi kasar nan don kawo sauki da kuma irin tasirin da rushewar wasu bankunan kasar Amurka za su iya yi a Nijeriya.

Sai dai, a nasa bangaren, masanin tattalin arziki a Nijeriya, Malam Yusha’u Aliyu, ya ce matakin na kwamitin manufofin kudi na bankin CBN zai kara hauhawar farashi ne kawai, yana mai cewa ana yin irin wannan karin ne don rage yawan kudi da ke yawo tsakanin al’umma, wanda bankin ya riga ya janye kudaden daga hannun al’umma.

LABARAI MASU NASABA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

Baya ga batun kara kudin ruwa, Emefiele ya bayyana cewa bankin ya goyi bayan hukuncin kotun koli na a ci gaba da mu’amala da tsoffin takardun kudi baya ga sabbin da aka sake fasalinsu wanda adadinsu ya kai kusan Naira tiriliyan daya.

Kazalika, Emefiele ya ce babban banki na da kwarin gwiwa a kan bankunan kasuwancin Nijeriya wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu ganin yadda suke ci gaba da jure wa asalin jarin da suka zuba na kaso 13 cikin 100, ba da lamuni wanda mutumin da ya karbin rance bai sanya lokacin fara biyansu ba na kaso 4.2 cikin 100 da kuma kudaden ajiyar bankunan da aka kara zuwa naira tiriliyan goma sha hudu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja
Manyan Labarai

Laftanal Yarima Ya Tsallake Rijiya Da Baya A Abuja

November 16, 2025
Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su
Manyan Labarai

Falana Ya Shawarci Waɗanda Suka Biya Kuɗin Fansa Su Kai Gwamnati Kotu Don Ta Biya Su

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Next Post
Zaben 2023 Ya Nuna Dimokuradiyyar Nijeriya Ta Bunkasa -Buhari

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

Fasinjojin Da Kasar Sin Ta Yi Jigilarsu Ta Jirgin Kasa Daga Janairu Zuwa Oktoba Sun Kai Biliyan 3.95

November 16, 2025
Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

Ƴan Bindiga Sun Sace Mutane 14 A Wani Sabon Hari A Zamfara

November 16, 2025
Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

Babban Jirgin Ruwan Yaki Samfurin 076 Na Sin Ya Kammala Gwajinsa Na Farko A Teku

November 16, 2025
Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

Sin Ta Gargadi Philippines A Kan Ci Gaba Da Tayar Da Zaune Tsaye A Tekun Kudancinta

November 16, 2025
An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

An Yi Taron Karatun Sinanci Na Duniya Na 2025 A Beijing

November 16, 2025
Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

Ana Mai Da Hankali Kan Dabarun Kasar Sin A Fannin Tinkarar Sauyin Yanayin Duniya A Taron COP30

November 16, 2025
Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

Wata Ƙungiya Ta Fara Bin Digdigin Takardun Karatun Matawalle

November 16, 2025
DSS

Hukumar DSS Ta Kama Wani Kan Zargin Ƙerawa Da Rarraba Makamai A Filato

November 16, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.