Babban Bankin Nijeriya CBN, ya umarci Daraktocin Bankunan kasar da suka ci bashin Bankunan suka gaza maido wa, da su sauka daga kan mukamansu nan take, ko kuma su yi murabus.
Wannan umarnin na CBN, na kunshe a cikin wata takarda da Mukaddashin riko na sashen kula da sanya ido na Bankin Adetona Adedeji, ya fitar a ranar Litinin da ta Litinin data gabata.
- An Bude Cibiyar Tattarawa Da Yada Labarai Ta Taruka Biyu Na Sin
- Gwamnatin Kano Za Ta Ɗau Nauyin Ɗalibai 1,002 Domin Karatu A Ƙasashen Waje
Bankuna ko kuma Cibiyoyin hada-hadar kudaden ne, ke bai wa manyan Shugabannin gudanar tafiyar da da Bankuna, Daraktocin Bankuna, ma’aikatan Bankuna, manyan masu ruwa da tsaki, a harkar Bankuna da sauransu, irin wannan bashin na kudaden.
A cewar Bankin na CBN, ya dauki wannan matakin ne, domin ya kara karfafa gudanar da tafiyar da Bankunan kasar da kaucewa, jefa Bankunan a cikin wata matsala.
Bankin ya ci gaba da cewa, ya dauki wannan matakin ne, daidai da sashe na 19 na tafiyar da Bankuna da gudanar da Cibiyoyin hada-hadar kudade, daidai da dokar BOFIA ta shekarar 2020, wacce ta umarci daukacin Bankunan kasar, da su tabbatar da sun wanzar da wannan umarnin, kan batun da ya shafi bayar da irin wannan rancen.
Bankin na CBN ya sanar da cewa, daukacin Bankunan, ana sa ran su bi wannan umarnin nan take.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp