Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya yi gargadi cewa zai ɗauki mataki mai tsauri kan bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi da ke karkatar da takardun Naira ta hanyoyin da ba su dace ba.
A cewar CBN, duk wani banki da aka samu da laifi zai fuskanci tara har naira miliyan 150, ko kuma hukunci mai tsanani, kamar yadda dokar BOFIA ta 2020 ta tanada.
- Firaminista Li Qiang Ya Shugabanci Taron Majalisar Gudanarwar Kasar Sin
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Aniyar Amurka Ta Sanya Karin Haraji Kan Wasu Hajojin Sin Dake Shiga Kasar
Sanarwar da CBN ya fitar ranar 13 ga watan Disamba, ta hannun Solaja Olayemi, mukaddashin daraktan kula da harkokin kuɗi, ta bayyana yadda wasu bankuna ke karkatar da takardun kuɗi maimakon su rarraba wa kwastomomi ko sanya su a ATM.
Wannan lamari, a cewar CBN, yana haddasa ƙarancin kuɗi a hannun mutane, sannan yana sa wasu suna dora wa gwamnati laifi.
CBN ya kuma ce zai fara sa ido kai tsaye ta hanyar ziyarar ba-zata zuwa dakunan bankuna da ATM a faɗin ƙasar, domin gano masu aikata wannan ɗabi’a da hukunta su.