Masanin tattalin arziki da ya lashe lambar yabon Nobel, Eric Maskin ya bayyana a wata hira da ya yi da babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG cewa, bude kofa ga kasashen waje da kuma zama daya daga cikin bangarorin tattalin arziki da kimiyya na kasa da kasa, sun sa kasar Sin ta samu sauyi sosai daga wata kasa mai fama da talauci shekaru 40 da suka gabata zuwa wata kasa mai wadata da saurin ci gaban tattalin arziki a yau.
Maskin ya ce, akwai sirrika da dama tattare da nasarar da kasar Sin ta samu. Na farko, kasar Sin na tafiyar da harkokin tattalin arziki irin na kasuwanci. Karfin kasuwa ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban tattalin arzikin Sin. Ban da haka kuma, bude kofa ga kasashen waje da kasar Sin take yi, shi ma wani muhimmin mataki ne mai dacewa. Haka kuma, tsarin gudanar da gwamnatin kasar Sin shi ma ya samu nasara matuka.
Kasar Sin tana da gwamnatin tsakiya, larduna da kananan hukumomi. Tattalin arzikin lardunan kasar Sin na da mabambantan halaye, kuma takara a tsakaninsu ta kara habaka tattalin arzikinsu. A karkashin wannan tsarin, kasar Sin na gudanar da ayyukan gwaji a wasu wurare, wanda hakan wani sirri ne na nasarar da kasar Sin ta samu. Ba shakka wannan kyakkyawan tunanin tattalin arziki ne. (Yahaya)