Kungiyar fafutukar kare dimokuradiyya (CDD), ta jinjina wa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da masu ruwa da tsaki bisa samun nasarar gudanar da zaben jihar Osun cikin kwanciyar hankali da nasara.
A jawabin bayan zabe da kungiyar ta fitar a ranar Lahadi dauke da sa hannun daraktanta, Idayat Hassan da shugaba sashen nazarin zabe na kungiyar CDD-EAC, Farfesa Adele Jinadu, ta jinjina wa dukkanin masu ruwa da tsaki bisa bada kokarinsu wajen yin zabe mai nagarta.
- Harin Jirgin Kasan Kaduna-Abuja: Gwamnatin Neja Ta Bukaci A Saki Matar Tsohon Gwamnan Kano Da ‘Ya’ya 5
- Hajjin 2022: Alhazan Bangladesh 88 Ne Suka Rasu A Saudiyya
CDD-EAC ta kuma nuna gamsuwa kan yadda aka fito aka yi zaben cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Haka nan sun kuma yaba da yadda aka gudanar da zaben jihar Ekiti a watan da ta shude.
Daga nan kungiyar ta bukaci wadanda suka shiga aka dama da su a yayin zaben da Allah bai basu nasara ba da su dauki dangana kana su mara wa wanda ya fi baya domin tabbatar da ingancin demokradiyya a kowani lokaci.
Kazalika bisa gabatowar babban zaben 2023, kungiyar ta bukaci INEC da ta yi kokarin dabbaka salo da dabarun da ya yi amfani da su a zaben Osun da Ekiti wajen gudanar da babban zaben 2023 da su domin tabbatar da an gudanar da zabukan cikin kwanciyar hankali da sahihanci.
CDD-EAC ta nemi masu zabe da suke kauracewa sayar da ‘yancinsu na sayar da kuri’unsu ga masu zabe.