Kungiyar kwallon kafa ta Chelsea ta bayyana cewa, kocin kungiyar Mauricio Pochettino ya ajiye aikinsa na horar da babbar tawagar kungiyar ayau Talata.
“Ina matukar godiya ga Chelsea da mahukuntanta akan damar da suka bani na jan ragamar wannan babbar kungiya zuwa wannan mataki da muke a yanzu,” in ji Pochettino.
- PSG Ta Shiga Gaban Chelsea Wajen Neman Daukar Victor Osimhen
- Chelsea Za Ta Fafata Da Real Madrid Da Manchester City A Amurka
Ana hasashen babu wata rashin fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu, kawai dai Chelsea na fatan ganin ta kawo wani sabon mai horaswa a kungiyar da zai ci gaba daga inda tsohon kocin na Tottenham da PSG ya tsaya.
Pochettino ya karbi aikin horarwa a Chelsea a farkon shigowar kakar bana inda ya jagoranci kungiyar ta Stamford Bridge da ta kare a mataki na 6 kuma ta samu damar buga UEFA Conference League a badi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp