Gwamnatin China ta gargaɗi Amurka da kada ta tsoma baki a harkokin Nijeriya, bayan Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar amfani da ƙarfin soji saboda zargin yi wa Kiristoci kisan gilla.
A taron manema labarai da aka gudanar a ranar Talata, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen China, Mao Ning, ta ce ƙasar “na goyon bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayin da ta ke jagorantar al’ummar Nijeriya bisa tafarkin ci gaba da ya dace da yanayin ƙasar.”
Ta bayyana Nijeriya a matsayin ɗaya daga cikin “abokan hulɗar China na ci gaba”, tare da tabbatar da cewa ƙasar za ta ci gaba da goyon bayan kasar Afrika ta Yamma.
“China na adawa da duk wata ƙasa da ke amfani da addini ko batun kare haƙƙin ɗan adam a matsayin hujja don tsoma baki a cikin harkokin wasu ƙasashe, ko kuma yin barazanar ƙaƙaba musu takunkumi ko amfani da ƙarfi,” in ji Mao.
Wannan jawabi ya biyo bayan gargaɗin da Trump ya yi kwanan nan cewa Amurka na iya amfani da karfin soja idan rahotannin cin zarafin addini a Nijeriya suka ci gaba da faruwa.
Matsayar da China ta ɗauka na nuna cikakken goyon bayanta ga gwamnatin Tinubu a lokacin da ƙasashen Yammacin duniya, musamman Amurka, ke matsa lamba kan batutuwan haƙƙin ɗan adam da tsaron cikin gida a Nijeriya.














