Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umurci mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima da ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa taron kasashe da suka taso karkashin mulkin mallakar Birtaniya da masu magana da yaren Turanci ‘Commonwealth’ na 2024 (CHOGM).
A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, Stanley Nwokocha, mai magana da yawun mataimakin shugaban kasar, ya ce Shettima zai hadu da Sarki Charles na Ingila da sauran shugabannin duniya daga kasashe mambobi 56 a taron CHOGM na farko da za a yi a tsibirin Apia na Pacific na Samoa daga ranar 21 zuwa 26 ga Oktoba.
- Yara Mata Miliyan 370 Ke Fuskantar Cin Zarafi Da Fyade A Duniya –UNICEF
- Da Ɗumi-ɗumi: APC Ta Lashe Zaɓen Ƙananan Hukumomin Kaduna
Ana sa ran, mahalarta taron za su tattauna kan makomar kungiyar da yadda za a tsira tare ta fannin habaka tattalin arzikin kasashen.
“A wannan taron, Nijeriya da sauran kasashe mambobi za su yi zabe tare da nada sabon Sakatare-Janar na Commonwealth.
“Wadanda za su fafata a wannan matsayi sun fito ne daga kasashen Lesotho, Ghana, da Gambia, yayin da Nijeriya za ta taka rawar gani a matsayin babbar mamba a Afirka a wannan kungiyar.” In ji Stanley