Ko da yake kasar Amurka ta hana kamfanonin Sin masu nasaba da fasahar kirkirarriyar basira (AI) samun na’urorin laturoni na Chips da Amurka din ta samar, kamfanonin Sin na ci gaba da samun dimbin nasarori a fannin fasahar AI.
A kwanan nan, kamfanin DeepSeek na kasar Sin ya samar da manhajar AI mai taken DeepSeek V3.2, wadda ta samu inganci iri daya da manhajojin GPT-5 da Gemini 3.0 Pro na kasar Amurka. Sai kuma Math-V2 da kamfanin DeepSeek ya tsara, ya cimma matsayin lambar zinariya a wata babbar gasar lissafi ta duniya. Kana Kimi K2 Thinking da kamfanin Moonshot AI na kasar Sin ya tsara, shi ma ya shahara a duniya, musamman ma tsakanin kwararru masu nazarin kimiyya da fasaha. To, wadannan nasarorin da kasar Sin ta samu tamkar mari ne a fuskar Amurka, ganin yadda Amurkar ke ta kokarin hana kasar Sin samun Chips din dake da matukar muhimmanci ga aikin raya fasahar AI.
Hakika idan an tantance jami’an kasar Amurka masu kula da manufar Chips, za a ga yadda suka kasance cikin rukunoni guda 2, inda rukuni na farko ke son ba kasar Sin wasu nau’ikan Chips, ta yadda Sin za ta fara dogaro kan fasahohin kasar Amurka. Daga baya, sai kasar Amurka ta rufe kofarta ga kasar Sin a duk lokacin da ta ga dama, don gurgunta bangaren AI na Sin.
Kana rukuni na biyu na jami’an Amurka na kallon hadin gwiwar da ake yi da kasar Sin a matsayin abu mai hadari, saboda haka suna neman daukar mataki mai karfi don hana kasar Sin samun Chips kirar kasar Amurka.
Sai dai nasarorin da kasar Sin ta samu ta fuskar fasahar AI sun shaida cewa, yunkurin dukkan rukunonin 2 na hana ta samun ci gaban fasaha ya ci tura.
To, me ya sa haka? Dalili shi ne, kasar Sin ta riga ta mallaki cikakken fifiko a bangaren raya fasahar AI.
Joseph Tsai, shugaban Alibaba, babban kamfanin kasar Sin mai kula da ayyuka masu alaka da shafin yanar gizo ko Intanet, ya bayyana fifikon Sin kamar haka:
Na farko, karfin da kasar ke da shi wajen samar da wutar lantarki.
Ci gaban fasahar AI yana bukatar amfani da dimbin wutar lantarki, lamarin da ya sanya kasar Sin samun fifiko, ganin yadda karfinta na samar da wutar lantarki ya ninka na kasar Amurka har sau 2.6, kana karuwar da Sin take samu a duk shekara, a fannin karfin samar da lantarki, ta ninka ta kasar Amurka har sau 9.
Na biyu, kudin da ake kashewa domin raya fasahar AI a kasar Sin ya fi araha. Misali, idan an kwatanta kudin da aka kashe domin gina wata cibiyar sarrafa alkaluma ta fasahar AI a kasar Sin da kasar Amurka, to, za a ga cewa, kaso 40 kacal kasar Sin za ta kashe na kudin da aka kashe a kasar Amurka.
Na uku, yadda kasar Sin ke mallakar dimbin kwararru.
Dimbin injiniyoyin da kasar Sin take da su sun tabbatar da karfin kasar a fannin kirkiro sabbin fasahohi, musamman ma a bangaren inganta fasahar AI. Hakika, kusan rabin kwararru masu nazarin fasahar AI na duniya sun taba karatu a jami’o’in kasar Sin.
Kana fifikon kasar Sin na hudu shi ne yadda kamfanonin kasar suka samar da damar yin amfani da manhajojinsu ba tare da bukatar biyan kudi ba, a kokarin taimaka wa karin kasashe da al’ummu. Saboda a ganin Sinawa, wanda zai ci nasara a gasar fasahar AI, shi ne wanda zai yi amfani da manhajojinsa wajen samar da hidimomi ga karin wurare, a karin fannonin rayuwa.
Har yanzu Amurkawa na neman hana kasar Sin samun ci gaban fasahar AI. Sai dai ta la’akari da yanayin da ake ciki yanzu, tabbas ba za a jima ba, za su fara rokon kasar Sin don samun damar hadin gwiwa da ita. (Bello Wang)














