• English
  • Business News
Saturday, October 11, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ci Gaban Kasar Sin Abun Koyi Ne Ga Kasashen Afrika

by CMG Hausa
2 years ago
Kasar Sin

Zaunannen wakilin Tarayyar Afrika (AU) a kasar Sin Rahamtalla Osman, ya ce kasar Sin ta kawo gagarumin sauyin wajen raya kanta, abun da ya zama misali ga kasashen Afrika.

Rahamtalla Osman ya bayyana haka ne yayin wata liyafa jiya a birnin Beijing, wadda kungiyar ’yan kasuwar Afrika mazauna kasashen ketare (ADBC) ta shirya, domin tattauna hanyoyin bunkasa ci gaban nahiyar Afrika.

  • Jakadun Kasashe 25 Sun Ce Ba Su Ga Abin Da Ake Kira “Aikin Tilastawa” A Xinjiang Ba

Jakadan na AU ya kara da cewa, Sin ta bude kofofinta ga kasashen Afrika da al’ummarsu, abun da ya kamata ya karfafa musu gwiwa wajen karfafa ci gaban nahiyar Afrika. Ya kara da cewa, AU tana karfafa hadin gwiwarta da Sin, lamarin da zai ba Afrika damar samun dabarun Sin na raya kanta da fatattakar talauci.

A nasa bangare, jakadan Nijeriya a kasar Sin Baba Ahmed Jidda, ya ce kyautata hadin gwiwar nahiyar Afrika da Sin, za ta kawo manyan sauye-sauye a nahiyar. Ya kara da cewa, yayin da taron BRICS ke karatowa a kasar Afrika ta Kudu a wannan wata, ya shawarci gwamnatin kasarsa ta yi amfani da wannan dama wajen cin gajiyar kungiyar har ma da kokarin zama mamba.

Shi kuwa shugaban kungiyar ADBC Kay Gabriel ya ce, (音响:英语 45秒)

LABARAI MASU NASABA

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

“Dalilin kafa wannan kungiya shi ne, karfafawa ’yan Afrika mazauna ketare gwiwar zuba jari da taimakawa kokarin da gwamnatocin Afrika ke yi wajen inganta zuba jari da samar da aikin yi ga matasa da yaki da talauci. A ganinmu, ’yan Afrika mazauna ketare na iya yin kyakkyawan tasiri a nahiyar ta hanyar amfani da wadatar da suke da ita. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne hada gwiwa da kwararru dake wajen nahiyar domin inganta sabbin kirkire-kirkire a Afrika.”

Bugu da kari, ya bukaci ’yan Afrika mazauna kasar Sin su kyautata hulda tsakanin Sin da kasashensu, haka kuma su yi kokarin jan hankalin ’yan kasuwar kasar domin su zuba jari a kasashen Afrika.

Liyafar ta jakadun Afrika dake kasar Sin, ta samu halartar jakadun kasashe da dama na Afrika dake kasar Sin, da ’yan kasuwa na Sin da Afrika da dalibai, da kwararru daga bangarorin biyu. (Fa’iza Mustapha)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza
Daga Birnin Sin

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025
Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya
Daga Birnin Sin

Sojojin Ruwan Sin Za Su Gudanar Da Aikin Sintiri A Zirin Tekun Aden Da Yankin Tekun Somaliya

October 10, 2025
CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa
Daga Birnin Sin

CMG Ya Kaddamar Da Shirin “Dabarun Tallata Kayayyakin Sin” A Tafarkin Gina Kasa Bisa Hadin Gwiwa

October 10, 2025
Next Post
Za Mu Tabbatar An Zakulo Makasan Sheikh Albani Kuri – Gwamnan Gombe 

Za Mu Tabbatar An Zakulo Makasan Sheikh Albani Kuri - Gwamnan Gombe 

LABARAI MASU NASABA

Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Sanatan Bauchi Ta Arewa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

October 11, 2025
Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba

Sojoji Da ‘Yansanda Sun Ceto Mutum Shida Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Taraba

October 11, 2025
Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara

Babban Kwamanda Ya Jagoranci Ceton Mutanen Da Aka Sace A Kwara

October 11, 2025
Yadda Jami’an ‘Yansanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja, Sun Kwashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

‘Yansanda Sun Tabbatar Da Mutuwar Wata Ba’amurkiya Da Ta Ziyarci Saurayinta A Jihar Delta

October 11, 2025
Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

Gwamnatin Osun Ta Horar Da Mata 500 Amfani Da Takin Gargajiya

October 11, 2025
Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano

Matasa 2 Sun Mutu Bayan Nutsewa A Rafi A Kano

October 11, 2025
Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

Dalilin IFAD Na Zuba Naira Biliyan 16 A Fannin Noma A Benuwe

October 11, 2025
Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

Yadda Haɗa Jinsin Shanu A Zamance Zai Ƙara Samar Da Madara

October 11, 2025
sallah

Gwamnatin Tarayya Ta Bukaci’ Yan Nijeriya Su Rika Sayen Kayan Da Aka Sarrafa A Gida

October 11, 2025
Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

Ma’aikatar Wajen Sin Ta Yi Tsokaci Kan Amincewar Da Isra’ila Ta Yi Da Yarjejeniyar Kawo Karshen Rikicin Gaza

October 10, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.