Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya sha alwashin cewa, za su bayar da dukkanin gudunmawa da goyon baya ga jami’an tsaro domin tabbatar da zakulo da kamo makasan babban malamin addinin Musluncin nan, Sheikh Ibrahim H. Musa Albani Kuri da ke jihar Gombe.
Idan za ku tuna dai LEADERSHIP Hausa ta bada labarin cewa wasu ‘yan bindiga dadi sun haura gidan Sheikh Albani Kuri da ke Tabra, anguwar dake gefen hanyar ratse ta Bypass Gombe tare da yi masa kisan gilla a daren ranar Laraba.
Gwamnan ya nuna matukar kadu da jin labarin rasuwar tare da shan alwashin daukan kwararan matakai na kamo makasan domin su fuskanci Shari’a.
Gwamna Inuwa wanda ya halarci sallar jana’izar marigayin a masallacin Izala da ke Bolari Gombe, ya yi tir da kakkausar murya kan wannan mummunan aika-aikar da ya ce ya girgiza al’amuran tsaro da zaman lafiya da ake da shi a Jihar Gombe.
“Mu na tabbatarwa al’ummar Jihar Gombe cewa gwamnati a tsaye take tsayin daka wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiyan al’ummarta, za mu ci gaba da daukan kwararan matakai ta hanyar amfani da karfin jami’an tsaronmu don kawar da masu aikata laifuka a duk inda suke a fadin jihar nan, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan danyen aikin a gaban kuliya don magance sake afkuwar irin haka.
“Wannan abu da ya faru ga Sheikh Ibrahim Albani Kuri zai zame mana hannunka mai sanda, cewa wajibi ne mu ci gaba da yin taka tsantsan da tsayin daka wajen samar da al’umma mai ci gaba, inda kowa zai iya rayuwa cikin aminci ba tare da tsoro ba”.
Ya kuma bukaci al’ummar jihar su ci gaba da hada kai cikin taimakekeniyar juna, tare da dabbaƙa dabi’un tausayawa da hadin kai wadda shugabanninmu na addinin suke ta kira a kai ba dare ba rana.
“Jama’ar jihar nan baki daya su na cikin alhinin kisan wannan malami, wadda koyarwarsa ta yi tasiri ga rayuwar al’ummar Musulmi da dama.”
Gwamna Inuwa ya ce marigayi Sheikh Ibrahim ya kasance mabubbugar ilimi, wadda ke karfafa fahimta da hadin kai, wanda koyarwarsa ta yi tasiri wajen ƙarfafa haɗin kan jama’a. Ya ce kowa zai ji zafin rashin wannan malami matuƙa, kuma abin da ya bari zai ci gaba da zaburar da al’umma a kullum.
Gwamnan a madadin gwamnati da al’ummar Jihar Gombe ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, da kuma kungiyar Izala da dokacin al’ummar musulmi bisa wannan rashi na bakin ciki. Ya yi addu’ar Allah Ta’ala ya saka masa da Aljannar Firdausi.