Guda daga cikin manyan jarumai, masu shirya fina-finan barkwanci da fadakarwa, Musa Mai Sana’a, ya bayyana abin da ya sani dangane da ci gaban da ake tunanin Masana’antar Kannywood ta samu, inda ya ce; ko shakka babu ganin kitse ake yi wa rogo, idan ana yin maganar ci gaba a wannan masana’anta ta shirya fina-finan Hausa.
A wata hira da aka yi da Mai Sana’ar, a gidan rediyon muryar Amurka, ya bayyana batutuwa da dama da suka shafi rayuwa da sauran al’amura na yau da kullum, tunda farko dai; jarumin ya yi bayani a kan yadda wasu lokutan yake samo labarun wasu daga cikin fina-finansa, don nishadantarwa ko fadakar da masu kallo.
- An Kammala Aikin Tsugunar Da Mutane A Gundumar Tingri Ta Sin Bayan Bala’in Girgizar Kasa
- AFCON 2025: Nijeriya Za Ta Fafata Da Tunisiya A Wasannin Rukuni
“Wasu lokutan, nakan tashi na tafi wani waje, wanda idan na fada; ba lallai a yarda ba. Misali, idan na so nishadi ko na dan bukaci yawon shakatawa, nakan tafi wurare kamar wajen da masu sana’ar Adaidaita Sahu ke tsayawa; su dan huta bayan sun yi aiki sun gaji, da sauran wurare da za ka ga rayuwa iri-iri, wanda hakan zai iya ba ka dama ka kwaikwayi abubuwan da ka gani; ka mayar da shi shirin fim, domin mutane su amfana; su kuma karu da ilimin zaman duniya”, in ji shi.
Da yake amsa tambaya kan yadda yake samo wasu ayoyi da hadisan da yake yawan amfani da su a fina-finansa, sai ya ce; duk da shi ba Malamin Addini ba ne, amma kuma Almajiri ne da ya yi karatun addini bakin gwargwado. Ya kara da cewa, ba Darakta ba ne yake rubuta masa wadannan ayoyi ko hadisai da yake karantowa a fim ba, kawai dai yana fadar su ne daga abin da ya koya a gaban Malamansa na addini.
Mai Sana’a ya ci gaba da bayyana cewa, dangane da abin da mutane ke fada cewa, gwamnatin tarayya ta yi matukar taka rawar gani ko ta sallami Masana’antar Kannywood, a kan gudunmawar da suka bayar a lokacin yakin neman zabe ta hanyar nada wasu daga cikin manyan jarumai manyan mukaman gwamnati, ko kusa ba haka abin yake ba; domin kuwa ba masana’antar aka sallama ba, illa kawai daidaikun wasu daga cikinsu.
Har ila yau ya ce, idan aka yi maganar mukaman da gwamnatin tarayya da ta jihohi suka bai wa wasu daga cikinmu, ba yana nufin cewa; an taimaki masana’antar ba ne, domin kuwa; mafi yawancin wadanda suka samu wadannan mukamai, babu wani ci gaba ko hobbasa da suka yi wajen ciyar da Masana’antar Kannywood gaba.
Musa ya ce, illa kawai dai suna taimakon kansu da kuma na kusa da su, wanda kuma ba haka ya dace a ce suna yi ba, dalili kuwa shi ne, har yau babu wani daga cikin masana’antar tamu da ya taba samun wani mukamin gwamnati, ya taimaka wa ita kanta masana’antar, illa kalilan daga cikinmu.
A bangaren abokanan fada kuwa a Masana’antar Kannywood, Mai Sana’a ya ce; duk da wannan magana da yake yi a halin yanzu, babu wani a masana’antar da zai bude baki ya ce; shi ne abokin fadansa, domin kuwa dukkanin wadanda suke tare a masana’antar, yana kallonsu da mutunci duk da cewa dai wasu sun fi wasu zama mutanen kirki.
A karshe, Musa ya bayyana cewa; idan Allah ya kawo wata sana’ar da ta fi wannan harka ta fim a wajensa, zai ajiye ta a cikin lumana; ba wai don ta yi masa tsaroro ba ba, kawai dai yana fatan wata rana wani abu daban zai zo, wanda ya fi masa harkar fim din, domin babu wani mutum a duniya da ba ya son cigaba, idan kuma wannan sana’a ita ce tsira a wajensa, yana fatan mutuwa a cikinta, ba tare da ya bar ta ba.