Cibiyar Ba da Agaji ta Sarki Salman na Saudiya ta kaddamar da aikin kiwon tiyatar cututtukan zuciya ga manya a Jihar Kano, inda tawagar likitocin sa kai guda 20 suka gudanar bisa hadin gwiwa da Kungiyar Kasashen Musulmi ta Duniya.
Tun daga lokacin da aka fara aikin, tawagar likitocin sa kai masu kishin kasa a cibiyar sun gudanar da gagarumin aikin tiyatar zuciya guda hudu da aka samu nasara a kai. A dukkan tiyatar da aka yi, likitocin sun nuna kwarewa da jin kai, lamarin da ya nuna kyakkyawan misali bisa dukufar da likitocin suka yi wajen warkar da marasa lafiya da kuma kara kwarin gwiwa ga mabukata.
Aikin dai ya zo ne a cikin tsarin tallafin da Masarautar Saudiya ta bayar ta sashen bayar da agaji na jin kan al’umma, watau cibiyar agaji ta Sarki Salman don tallafa wa fannin kiwon lafiya a Nijeriya, da kuma kafa tsarin gudanar da aiki na sa kai a tsakanin al’ummar Saudiyya, bisa manufofin da masarautar ta sa gaba da ake son cimmawa nan da 2030.
Wannan hadin gwiwa ya zama shaida ga irin karfin da hadin kai yake da shi na samar da sauki a lokacin ibtila’i, inda kungiyoyi da hukumomin da ke da nisa da juna za su rika hada karfi don sauya rayuwar jama’a bila’adadin.
A yayin da aka kaddamar da aikin kiwon lafiyar na sa kai a Jihar Kano, hakan ya nuna kyakykyawan tausayi da jin kan bil’adama lokacin ibtila’i. A duk tiyatar zuciyar da aka yi, an rubuta bayanan sauyin da aka gani, wanda ke nuna babban tasiri da alherin da masarautar ta Saudiyya take aiwatarwa a Nijeriya.
Idan dai za a iya tunawa, a watan Yuni ne masarautar Saudiyya ta kuduri aniyar samar da cibiyar tiyatar zuciya a Kano domin rage radadin rashin lafiyar da ke bukatar tiyatar bugun zuciya a kasar.
Khalid Ahmad Al-adamawi, karamin jakadan Saudiyya a Nijeriya, wanda ya ziyarci Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano, ya yi wa gwamnan bayani dangane da aikin tiyatar zuciyar da ake yi a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH).
A kwanakin baya ne dai Cibiyar Bayar da Agaji ta Sarki Salman ta kudiri aniyar samar da aikin jinya na sa-kai domin kula da masu cutar yoyon fitsari a jihar Kano. Inda daga ranar 6 zuwa 11 ga Agusta 2023, likitocin sa kai suka gudanar da aikin tiyata 65.
Gidauniyar tana aiwatar da jerin shirye-shirye da tsare-tsare don samar wa marasa lafiya a duk fadin duniya da ingantaccen magani da sauran harkokin kiwon lafiyar da ba a samu a yankunan jama’ar da ake yi wa.