Tun lokacin da aka fara gudanar da baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin ko CIIE a takaice a shekarar 2018, kasashe masu halartar baje kolin na shekara-shekara sun yi amfani da tasirin girmar kasuwar kasar Sin, wanda ya kasance dandalin hada-hadar cinikayya na kasa da kasa, da inganta zuba jari, da mu’amalar jama’a da yin hadin gwiwa, da ba da gudummawa mai kyau wajen samar da sabbin tsarin ci gaba, da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya.
La’akari da tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin duniya ke yi biyo bayan rashin cikakkiyar farfadowa daga tasirin annobar COVID 19, shugaba Xi Jinping a cikin wasikarsa na bikin bude baje kolin a jiya Lahadi ya ce, kasar Sin za ta kasance wata muhimmiyar dama ta ci gaban duniya a ko da yaushe, kuma za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen waje, da kuma ci gaba da sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya, ta hanyar ci gaba da inganta baje kolin na kayayyaki da ake shigowa da su kasar daga kasashen waje.
- Kasar Sin Za Ta Ci Gaba Da Yin Iyakar Kokarin Saukaka Rikicin Gaza
- Xi Jinping Ya Taya Murnar Gudanar Da Babban Taron Birane Masu Sada Zumunta Na Sin Da Amurka
Baje kolin CIIE na bana ya jawo hankalin mahalarta daga kasashe, yankuna da kungiyoyin kasa da kasa 154. Sama da masu baje kolin 3,400 da kwararrun baki 394,000 suka yi rajista don halartar taron, wanda ke nuni da cikakkiyar karbuwar baje kolin.
Daga cikin kamfanoni 3,000 na duniya dake halartar baje kolin na wannan shekara, kusan kamfanoni 200 ne suka halarci baje kolin tun daga shekarar 2018 har ya zuwa yanzu, kuma kusan kamfanoni 400 ne ke dawowa baje kolin bayan duk shekaru biyu.
Yawancin kamfanonin kasashen waje da ke gudanar da kasuwanci a kasar Sin suna da kwarin gwiwa game da ci gaba da gudanar da kasuwancinsu a kasar, inda sama da kashi 90 cikin 100 na wadannan kamfanonin suna sa ran za su maido da jarinsu ko ribar da suke samu zai karu a cikin shekaru biyar masu zuwa ko kasa da haka, a cewar wani bincike na baya-bayan nan da Majalisar Bunkasa Harkokin Cinikayya ta Duniya ta gudanar a kasar Sin.
Binciken ya kuma nuna cewa, kamfanonin kasashen waje sun nuna kwarin gwiwar fadada hada-hadarsu na kasuwanci a kasar Sin, yayin da sama da kashi 70 cikin 100 na wadanda suka amsa tambayoyin binciken suka ce za su dawo da wasu sassan masana’antunsu kasar Sin.
Alkalumma a hukumance sun nuna cewa, hada-hadar kayayyakin da kasar Sin ke shigowa da su kasar na ci gaba da tafiya yadda ya kamata, inda yawan kayayyaki da take shigowa da su ya karu a kowane rubu’i na bana. Kasar Sin ta kasance kasa ta biyu a fannin shigo da kayayyaki a duniya tsawon shekaru 14 a jere.
“Baje kolin ya nuna cewa, kasar Sin a bude take don yin kasuwanci da sauran kasashen duniya. Wannan wata babbar dama ce ga kasashe daban-daban su yi baje kolin hajojinsu da fasahohinsu.”
Baya ga bayar da damammaki ga kasashe masu tasowa da kasuwanni masu tasowa, baje kolin CIIE ya kasance dandalin sada zumunta da kamfanonin kasar Sin ta hanyar yin hadin gwiwa da kamfanonin kasashen waje don samar da kayayyaki ko ayyuka ga kasuwannin kasar Sin ko na duniya baki daya. (Muhammed Yahaya)