Sufeto Janar na Ƴansanda, IGP Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa rundunar ƴansandan Nijeriya ta kama mutane 5,488 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban tare da ceto mutane 170 da aka sace a faɗin ƙasar nan tsakanin watan Yuni da Yuli na shekarar 2025.
IGP Egbetokun ya bayyana haka ne a lokacin wani taron dabarun tsaro da ya gudana a Abuja tare da Mataimakan Sufeto Janar (DIGs), Kwamishinonin Ƴansanda (CPs), da Kwamishinonin Yanki (AIGs), kamar yadda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya bayyana a cikin wata sanarwa.
- Jerin Manyan Jaruman Fim Da Nijeriya Ta Rasa A Yan Shekarun Nan
- Ƴan Bindiga Sun Yi Wa Jami’an NSCDC Ƙwantan Ɓauna A Binuwe
IGP ɗin ya ce rundunar tana ƙara zage damtse wajen gudanar da bincike bisa leƙen asiri da kuma haɗin gwuiwa da al’umma don tunkarar barazanar tsaro da ke ƙara sauyawa a ƙasar.
A cewarsa, “A tsakanin watan Yuni zuwa Yuli 2025 kaɗai, mun kama mutane 5,488 da ake zargi da laifuka kamar garkuwa da mutane, da fashi da makami, da rikicin ƙungiyoyi da kuma kisan kai.”
Binciken ya kuma nuna cewa a cikin waɗannan watanni biyu, ƴansanda sun ƙwato bindigogi 316, da harsasai 2,884, da motoci 216 da aka sace ko ba su da rajista a yayin gudanar da ayyuka a sassa daban-daban na ƙasar.
IGP ya yabawa tawagar Interpol reshen Nijeriya bisa ceto Ghanawa 46 da aka yi safararsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp