Kasar Sin ta sanar da daukar matakan rage salwantar abinci domin samar da wani tsari mai dorewa na dakile hakan zuwa karshen shekarar 2027.
Shirin zai mayar da hankali wajen rage yawan hatsi da abincin dake salwanta, tun daga matakin samarwa zuwa adanawa da jigila da sarrafa abincin, zuwa kasa da mizanin kasa da kasa, ya zuwa karshen 2027.
Wannan shiri na Sin, ya yi daidai da ajandar MDD ta 2030 ta rage salwantar abinci, haka kuma zai zama abun koyi da duba ga sauran kasashen duniya musamman masu tasowa, domin a duk lokacin da abinci ya salwanta, to ya rage wadatar abincin kuma ya haifar da asarar albarkatun da aka zuba kamar ruwa, taki, kudi da ma karfin da aka sanya wajen samar da shi. Baya ga haka, zubar da abinci ko kona shi cikin shara, na kara yawan hayaki mai dumama yanayi da ake fitarwa, wanda ke mummunan tasiri ga yanayi da muhallin halittu.
Galibin mutane ba su dauki zubar da abinci a matsayin mummunan abu ba, sai dai illar hakan ta zarce tunanin mutum. A cewar MDD, ton biliyan 1.3 na abinci ne ke salwanta a kowacce shekara, yayin da mutane miliyan 135 ke fuskantar tsananin yunwa.
Hakika wannan mataki da Sin ta bullo da shi da zai hada da wayar da kan jama’a da rage asarar abinci a masana’antar sayar da abinci da dakunan cin abinci a ma’aikatun da hukumomi da makarantu da kuma karfafa tattara alkaluman da suka shafi salwantar abinci, zai bada gagarumar gudunmawa ga wadatuwar abincin da ma kyautata muhalli. Yayin da ya rage shekaru 12 wajen cimma burin MDD na rage salwantar abinci, tabbas Sin za ta kai ga cimma wannan manufa. Kana kamar yadda ta cimma fatattakar talauci da samar da abun koyi ga duniya, nasarar da za ta samu a wannan bangare ma zai zama abun koyi a duniya. Kuma hakan zai taimakawa kasashe wajen samar da dabarun rage radadin yunwa da tsadar abinci da samar da wadatar abincin, domin ta kasance jagora wajen samar da mafita ga matsalolin duniya musamman na kasashe masu tasowa. (Fa’iza Mustapha)