Kasashen Sin da Saudiyya da Iran sun fitar da hadaddiyar sanarwar bangarori uku a yammacin ranar 10 ga wannan wata, lamarin da ya ja hankalin kafofin watsa labarai na fadin duniya matuka. A cikin sanarwar, kasashen nan uku sun sanar da cewa, Saudiyya da Iran sun daddale yarjejeniya, inda suka amince da dawo da huldar diplomasiyya a tsakaninsu, kuma za su sake bude ofisoshin jakadancin su a kasashen juna, kana za su tura jakadunsu, tare kuma da tattaunawa game da yadda za su kara karfafa huldar dake tsakaninsu, a cikin watanni biyu masu zuwa. Kana kasashen uku sun bayyana cewa, za su yi kokari matuka domin kara karfafa kwanciyar hankali da tsaro a yankunan kasa da kasa.
Kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun yaba da batun a kan lokaci, kuma kasashen yankin Gabas ta Tsakiya, musamman ma Iraki da Oman da Lebanon da sauransu, sun yi maraba da sakamakon da aka cimma a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Shi ma babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya godewa kasar Sin saboda kokarin da ta yi na ingiza tattaunawa tsakanin Saudiyya da Iran, yana mai cewa, lamarin zai taimakawa kwanciyar hankali a yankin Gulf.
An lura cewa, kasashen duniya da dama sun taba yin kokarin yin sulhu tsakanin kasashen Saudiyya da Iran a cikin shekaru bakwai da suka gabata, amma ba su samu ci gaba a bayyane ba. Don haka ci gaban da aka samu a wannan karo, ya ba kafofin watsa labarai mamaki. (Mai fassarawa: Jamila)