Ministan Kasafi Kudi da Tattalin Arzik, Alhaji Abubakar Atiku Bagudu, ya bayyana cewa, cin bashi don karafafa kasafin kudi ba sabon abu ba ne a Nijeriya, ya bayyana haka ne a tattauanwarsa da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan taron majalisar kasa da aka yi ranar Litinin.
Ya ce, “Mun sa lissafin cewa, gangan mai za ta kama wajen dala 74, kuma muna ganin ingantgar tsaro da ake samu da kuma ingantar masu zuba jari da ake samu a bangaren hako man fetur ya sa aka samu bunkasa hako mai zuwa ganga wajen miliyan 1,780,000, kuma ana sa ran farashin kayyaki zai fara saukowa saboda matakan nan da ake dauka, amfaninsu zai fara zuwa nan gaba kadan , da wanna ne muka yi lissafi, cewa in Allah ya sa muka yi nasara abin da muke so za a yi kasafin kudi na Triliyan 26 da biliyan 10.
- Majalisar Wakilai Za Ta Amince Da Kasafin Kudin 2024 Kafin Karshen Disamba
- Na Sha Alwashin Magance Talauci Da Kashi 80 Cikin 100 A Jihata – Gwamnan Kaduna
Da aka tambaye shi a kan shirin gwamnati na ciwo bashin Dala biliyan 1 da rabi sai bayyana cewa, “Dala biliyan 1 da rabi, tallafi ne daga cikin kudin da ake nema kasafin kudin 2023. Ya kamata mu fahimci cewa, cikin shekara 11 duk wani masanin da ya duba kasafin kudin Nijeriya zai ga kudin da ke shigowa kadan ne bisa ga abin da ake kashewa, wato kowacce shekara sai mun ci bashi, alallmisali wannan shekara da muke ciki 2023 kasafin kudin da aka yi, abin da aka duba ya shigo wajen tirilyan 10 amma da aka lissafa za a kashe tiliyan 21 haka bara haka bara da bara wancan, kusan shekara 9 idan mutun ya duba tunda abin akwa ishi zai ga kowacce shekara sai an ci bashi.
To ba abin mamaki ba ne, kasashe kan shiga cikin wannan halin, lokacin da ake da wadata ba a yi tunani karfafa tattalin arziki ba, kuma banda wannan, lalurori daban daban sun samu duniya, kasashe da dama suna cikin wannan halin , an samu shekara biyu na cutar annobar korona wanda ta tagayyara duniya, an samu abin da ake kira ‘Ressesion’ wato raguywar kasuwanci a cikin duniya, abin da ya shafi kowa, yau akwai wuraren da ake yaki ba ma wuri daya ba abu ne da ya shafi kowa, yau kasuwanni da yawa ba sa hadahada, irin wannan ne ke mayar damu baya. Kudaden da NNPC ke cirewa don bayar da mai da rahusa,”
Ya kuma kara da cewa, Allah ya sa an gyara wannan kuma an kawo wasu lalurori a cikin al’umma wanda sai da aka tanadi kudaden da za a tallafa wa al’umma kamar dai yarjejeniyar da aka yi da kungiyoyin ma’aikata.
Daga karshe ya ce, shugabankasa bola Tinubu zai gabatar da kasafin kudi don cike ayyukan da za a kammala a cikn wannan shekarar wadanda ba za a iya kamalawa kujma sai a sa su cikin kasafin shekarar 2024, ta haka kasafin kudin Nijeriya zai ci gaba da tafiya bai-daya.