Sakatariyar kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) ta ki cewa uffan kan batun da gwamnatin tarayya ta kai karar gwamnonin jihohin tarayya 36 a gaban kotun koli bisa zargin rashin sakar wa kananan hukumomi mara.
Lokacin da aka tuntubi, Babban Daraktan NGF, Dakta Abdulateef Shittu ya bayyana cewa sakatariyar ta karanta rahoton, ya ce tun da dai batun ya riga ya shiga kotu, musamman kotun koli, zai iya magana a kai ba.
- Gwamnoni 9 Da Har Yanzu Ba Su Babe Da Iyayen Gidansu Ba
- Rikicin Masarautar Kano: Lauyoyi Da Alƙalai Sun Tozarta Ɓangaren Shari’a – Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi
Ya ce, “Sakatariyar NGF tana sane da cewa gwamnatin tarayya ta dauki matakin shari’a kan gwamnonin jihohi 36 na tarayya a gaban kotun koli bisa zargin rashin sakar wa kananan hukumomin mara ta yadda za su dunga cin gashin kansu. Tun da al’amarin yana gaban kotu, ba za a iya cewa komin ba har sai kotun koli ta zartar da hukuncinta. ”
Idan dai za a iya tunawa, gwamnatin tarayya ta shigar da kara a gaban kotun koli a kan gwamnonin jihohin kasar nan 36 bisa zargin tauye hakkin kananan hukumomin.
Gwamnatin tarayya a cikin karar da ta shigar mai lamba: SC/CB/343/2024, wadda babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya shigar, na neman cikakken ‘yancin cin gashin kai ga daukacin kananan hukumomin kasar nan a matsayin matakin gwamnati na uku.
Ta kuma bukaci kotun kolin da ta ba da umarni kan wannan lamarin tare da haramta wa gwamnonin jihohi yin rusa shugabannin kananan hukumomi ba bisa ka’ida ba.
Kazalika, gwamnatin tarayya tana bukatar kotun kolin ta bayar da izinin tura kudaden kananan hukumomi kai tsaye daga asusun tarayya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada wanda ya saba wa asusun hadin gwiwa da gwamnoni suka yi.