An yi kiyasin cinikayyar amfanin gona ta intanet a kasar Sin, ta karu da kaso 10 a shekarar 2022, yayin da bangaren aikin gona ke kara rungumar cinikayya ta intanet dake bunkasa a kasar.
Jami’in ma’aikatar kula da aikin gona da harkokin karkara ta kasar Sin, Zeng Yande, ya ce habakar masana’antar sarrafa amfanin gona a kasar ce ta ingiza bunkasar cinikayyarsu ta intanet. Yana mai cewa, an yi kiyasin wannna masana’anta za ta samar da karuwar kudin shigar manyan kamfanoni da kimanin kaso 4 a shekarar 2023.
A cewarsa, an gina wurare sama da 16,000 na adanawa da sanyaya amfanin gona a kasar a bara.
Alkaluman da hukumomi suka fitar jiya Talata, sun nuna cewa, cinikayya ta intanet a kasar Sin ta karu da kaso 4 a shekarar 2022 zuwa kusan yuan triliyan 13.8, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 2, wadda ta karfafa matsayin kasar na kasancewa ta 1 a fannin cinikayya ta intanet a duniya.(Fa’iza)