Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta ce kudaden cinikayyar waje na hajojin kasar Sin, sun karu da kaso 8.6 bisa dari, tsakanin watannin Janairu zuwa Nuwamban bana, inda darajar su ta kai kudin Sin yuan tiriliyan 38.34, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 5.78.
Alkaluman da hukumar ta fitar a Larabar nan, sun nuna karuwar hajojin da Sin ke fitarwa zuwa ketare da kaso 11.9 bisa dari, inda darajar su ta kai yuan tiriliyan 21.84, yayin da adadin hajojin da ake shigowa da su kasar suka karu da kaso 4.6 bisa dari, inda darajar su ta kai yuan tiriliyan 16.5.
Kaza lika, tsakanin watannin Janairu zuwa Nuwamban bana, cinikayyar Sin da kasashe mambobin kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya ya karu da kaso 15.5 bisa dari, ta tsakanin ta da kasashen tarayyar Turai ma ta karu da kaso 7 bisa dari, kana na tsakanin ta da Amurka ta karu da kaso 4.8 bisa dari.
Har ila yau, tsakanin wannan wa’adi, darajar cinikayyar Sin da kasashen dake cikin shawarar “ziri daya da hanya daya” ta karu da kaso 20.4 bisa dari, inda darajar cinikayyar ta kai yuan tiriliyan 12.54. (Saminu Alhassan)