• English
  • Business News
Monday, November 3, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da sabuwar kididdiga kan harkokin cinikin waje, inda aka nuna cewa, a watan Mayun bana, jimillar kudaden shige da fice na kasar Sin ta kai dala biliyan 537.74, wadda ta karu da kaso 11.1 bisa dari. Duk da cewa annobar COVID-19 na ci gaba da yaduwa, amma harkokin cinikin waje na kasar Sin, sun bunkasa yadda ya kamata tun daga watan Janairu zuwa Mayun bana, al’amarin da ya sake nunawa duniya babban kuzari da kwarewar kasar Sin.

Kwararan shaidu sun tabbatar da cewa, tasirin annobar na gajeren lokaci ne, kana, manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa, wato dakile yaduwar cutar da zarar an gano ta, gami da sauran wasu muhimman matakan kandagarkin yaduwar cutar da raya tattalin arziki sun taka rawar a-zo-a-gani.

Harkokin cinikin waje za su iya bayyana yadda tattalin arzikin kasar Sin yake gudana. A watanni biyar da suka gabata, kasar ta cimma tudun-dafawa wajen bunkasa cinikin waje, abun dake karfafa gwiwar duniya baki daya.

Duk da rashin sanin tabbas game da yaduwar cutar COVID-19 a halin yanzu, babban burin gwamnatin kasar Sin a fannin dakile yaduwar cutar shi ne, yin namijin kokari wajen kare rayuwar al’umma gami da lafiyarsu, da rage illolin da cutar ke haifarwa ga tattalin arziki da rayuwar al’ummar kasar. Tun daga gwamnatin kasa har zuwa kananan hukumomi, tun daga gwamnati har zuwa kamfanoni, duk dan kasar na kokarin ganin an cimma wannan burin.

Kasar Sin tana da kwarewa wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikinta yadda ya kamata, da ci gaba da bayar da muhimmiyar gudummawa wajen samar da kayayyaki da farfado da tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)

LABARAI MASU NASABA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar
Daga Birnin Sin

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
Daga Birnin Sin

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
Daga Birnin Sin

Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik

November 2, 2025
Next Post
Cutar Sanƙarau Ta Halaka Kusan Mutum 100 A Jigawa

Cutar Sanƙarau Ta Halaka Kusan Mutum 100 A Jigawa

LABARAI MASU NASABA

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

Kwankwaso Ya Gargaɗi Trump Kan Barazana Ga Nijeriya

November 2, 2025
Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

Gumi Ya Nemi Nijeriya Ta Katse Hulɗa Da Amurka Idan Trump Bai Janye Barazanar Sa Ba

November 2, 2025
Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

Shugaba Xi Ya Mika Sakon Taya Murnar Bude Babban Gidan Tarihi Na Kasar Masar

November 2, 2025
Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

Ƙasashen Da Ba Su Yanke Hukuncin Kisa A Duniya Ba

November 2, 2025
Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik

November 2, 2025
Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

Yadda Za Ku Hada Fab Biskit

November 2, 2025
Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

Kano Pillars Ta Koma Matsayi Na 20 Bayan Shan Kashi A Hannun Enyimba

November 2, 2025
Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

Wolves Ta Kori Da Kocinta Vitor Pereira Sakamakon Rashin Nasara

November 2, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

2027: Yadda Gwamnoni Suka Yi Fatali Da Mataimakansu Wajen Zaɓo Waɗanda Za Su Gaje Su

November 2, 2025
Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

Gidauniyar IRM Da KADCHMA Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna

November 2, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.