• Leadership Hausa
Wednesday, September 27, 2023
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Sana’a Sa’a
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata

by CMG Hausa
1 year ago
in Daga Birnin Sin
0
Cinikin Waje Na Kasar Sin Ya Bunkasa Yadda Ya Kamata
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da sabuwar kididdiga kan harkokin cinikin waje, inda aka nuna cewa, a watan Mayun bana, jimillar kudaden shige da fice na kasar Sin ta kai dala biliyan 537.74, wadda ta karu da kaso 11.1 bisa dari. Duk da cewa annobar COVID-19 na ci gaba da yaduwa, amma harkokin cinikin waje na kasar Sin, sun bunkasa yadda ya kamata tun daga watan Janairu zuwa Mayun bana, al’amarin da ya sake nunawa duniya babban kuzari da kwarewar kasar Sin.

Kwararan shaidu sun tabbatar da cewa, tasirin annobar na gajeren lokaci ne, kana, manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa, wato dakile yaduwar cutar da zarar an gano ta, gami da sauran wasu muhimman matakan kandagarkin yaduwar cutar da raya tattalin arziki sun taka rawar a-zo-a-gani.

Harkokin cinikin waje za su iya bayyana yadda tattalin arzikin kasar Sin yake gudana. A watanni biyar da suka gabata, kasar ta cimma tudun-dafawa wajen bunkasa cinikin waje, abun dake karfafa gwiwar duniya baki daya.

Duk da rashin sanin tabbas game da yaduwar cutar COVID-19 a halin yanzu, babban burin gwamnatin kasar Sin a fannin dakile yaduwar cutar shi ne, yin namijin kokari wajen kare rayuwar al’umma gami da lafiyarsu, da rage illolin da cutar ke haifarwa ga tattalin arziki da rayuwar al’ummar kasar. Tun daga gwamnatin kasa har zuwa kananan hukumomi, tun daga gwamnati har zuwa kamfanoni, duk dan kasar na kokarin ganin an cimma wannan burin.

Kasar Sin tana da kwarewa wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikinta yadda ya kamata, da ci gaba da bayar da muhimmiyar gudummawa wajen samar da kayayyaki da farfado da tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)

Labarai Masu Nasaba

Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya

Babban Jami’in JKS: Kasar Sin Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Amincewa Da Juna Da Kasar Masar

ShareTweetSendShare
Previous Post

Da Abokin Daka Akan Sha Gari

Next Post

Cutar Sanƙarau Ta Halaka Kusan Mutum 100 A Jigawa

Related

Duniya
Daga Birnin Sin

Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya

5 hours ago
JKS
Daga Birnin Sin

Babban Jami’in JKS: Kasar Sin Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Amincewa Da Juna Da Kasar Masar

6 hours ago
Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa

7 hours ago
Kimiyya
Daga Birnin Sin

Masana Kimiyya Na Kasashen Kenya Da Sin Sun Kaddamar Da Kundin Farko Game Da Nau’ikan Tsirran Da Kenya Ta Wallafa

8 hours ago
Libya
Daga Birnin Sin

Me Ya Haifar Da Ambaliya A Libya?

9 hours ago
Xi
Daga Birnin Sin

Xi Ya Jaddada Gina Ingantattun Yankunan Cinikayya Maras Shinge Na Gwaji

10 hours ago
Next Post
Cutar Sanƙarau Ta Halaka Kusan Mutum 100 A Jigawa

Cutar Sanƙarau Ta Halaka Kusan Mutum 100 A Jigawa

LABARAI MASU NASABA

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe

Hatsaniya Ta Kaure Kan Zargin Cirewa Wata Gawa Ido Daya A Asibitin Kwararru Da Ke Gombe

September 26, 2023
NNPP Ta Yi Watsi Da Hukuncin Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano Da Ta Ba Gawuna Nasara

NNPP Ta Kai Korafinta Ga Hukumar NJC Kan Kalaman Daya Da Cikin Alkalan Kotun Zaben Kano

September 26, 2023
Duniya

Ra’ayin Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makoma Ta Bai Daya Na Tattaro Karfin Sauya Duniya

September 26, 2023
‘Yansanda Sun Dakile Harin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Kan Wasu Rukunin Gidaje A Katsina

‘Yansandan Jihar Nasarawa Ta Tabbatar Da Sace Wasu Daliba A Jihar

September 26, 2023
JKS

Babban Jami’in JKS: Kasar Sin Za Ta Karfafa Hadin Gwiwa Da Amincewa Da Juna Da Kasar Masar

September 26, 2023
Kungiyar Kwadago (NLC) Na Shirin Tsunduma Wani Sabon Yajin Aiki Mai Dogon Zango

NLC Da TUC Sun Shirya Tsunduma Yajin Aiki Mai Dogon Zango Ranar Talata 3 Ga Oktoba 2023

September 26, 2023
Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa

Kasar Sin Mai Burin Ganin Ci Gaban Kowa

September 26, 2023
Da Alamun SAKA Ba Zai Buga Wasa Biyu Ba Saboda Raunin Da Ya Samu Arteta

Da Alamun SAKA Ba Zai Buga Wasa Biyu Ba Saboda Raunin Da Ya Samu Arteta

September 26, 2023
Kimiyya

Masana Kimiyya Na Kasashen Kenya Da Sin Sun Kaddamar Da Kundin Farko Game Da Nau’ikan Tsirran Da Kenya Ta Wallafa

September 26, 2023
Libya

Me Ya Haifar Da Ambaliya A Libya?

September 26, 2023
Advertise with us

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2022 Leadership Media Group - All Right Reserved.