Cinikin kayayyaki na kasar Sin ya ci gaba da samun habaka ba tare da tangarda ba a cikin watanni 10 na farkon wannan shekarar, inda ya kai yuan tiriliyan 37.31 (kwatankwacin dala tiriliyan 5.24), wanda ya karu da kashi 3.6 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara, kamar yadda bayanan da Hukumar Kwastam ta kasar Sin ta fitar a yau Jumma’a suka bayyana.
A watan Oktoba kadai, jimillar cinikin kayayyaki na kasar Sin ta karu da kashi 0.1 cikin dari a mizanin shekara-shekara zuwa yuan tiriliyan 3.7 (dala biliyan 519.7). Kayayyakin da ake shigowa da su daga waje sun karu da kashi 1.4 cikin dari, wanda hakan ya nuna an samu karuwarsu a cikin watanni biyar a jere.
Abin lura game da hakan shi ne, daga watan Janairu zuwa Oktoba, kasuwancin da kasar Sin ke yi da kasashen da ke bin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya (BRI) ya karu da kashi 5.9 cikin dari a mizanin shekara-shekara zuwa yuan tiriliyan 19.28 (dala tiriliyan 2.71). (Abdulrazaq Yahuza Jere)














