Gwamnatin jihar Kano ta rattaba hannu da kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC da TUC) kan yarjejeniyar fara bayar da tallafin Naira 20,000 ga daukacin ma’aikatan jihar.
An amimce da kudirin ne da nufin rage kalubalen matsin tattalin arziki da ma’aikatan gwamnati ke fuskanta a jihar Kano bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi.
- Jerin Jami’o’i 18 Da NUC Ta Haramta Karatu Acikinsu
- Hukumar Kashe Gobara Ta Kano Ta Ceto Rayuka 417 Da Dukiyoyin Nairori A Shekarar 2023
Shugaban kungiyar TUC reshen Kano, Kwamared Mubarak Buba Yarima ne ya tabbatar wa LEADERSHIP wannan rahoton, inda ya jaddada muhimmiyar rawar da kungiyoyin kwadago ke takawa wajen tattaunawa da gwamnati.
Yarjejeniyar ta samu nasara ne biyo bayan rokon haɗin gwiwa da NLC da TUC suka gabatar wa gwamnatin jihar Kano a watan Oktoban 2023, inda suka nemi gwamnatin da tallafawa ma’aikata kan mawuyacin halin da suke ciki.
Gwamna Yusuf, nan take ya kafa kwamiti na musamman domin nemo mafita kan kudurin. Sakamakon binciken da kwamitin ya gabatar, an cimma matsaya kan cewa za a fara biyan tallafin Naira N20,000 daga watan Disambar 2023 ga daukacin ma’aikatan gwamnati a matakin jihohi da kananan hukumomi.
Yarima ya kara da cewa, za a ci gaba da bayar da tallafin kudi har sai an gudanar da cikakken nazari kan mafi karancin albashi a cikin watanni shida masu zuwa.
Bugu da kari, masu karbar fansho za su rika karbar N15,000 duk wata na tsawon watanni uku, tare da biyan bashin alawus din Disamba 2023 da ba a biya ba.
Yarima ya bayyana jin dadinsa ga gwamnatin jihar Kano, musamman ma mai baiwa gwamna shawara kan harkokin kwadago, Kwamared Baffa Sani Gaya, da sauran mambobin kwamitin bisa wannan gagarumin bincike da suka mika wa gwamnatin.