Gwamnan Jihar Jigawa Umar Namadi, ya ce sun gama tanadin taimaka wa monama a jihar domin rage musu radadin cire tallafin man fetur da aka yi.
Cikin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da BBC Hausa, Gwamnatin Namadi, ya ce matakin farko da suka dauka shi ne rage farashin takin zamani daga naira “dubu 26 zuwa dubu 16”.
- Wutar Daji Ta Raba Mutane Dubu 30 Da Gidajensu A Girka
- Bidiyon Dalar Ganduje: Kotu Za Ta Yanke Hukunci Ranar 22 Ga Satumba
Gwamnan, ya ce suna sane da irin kalubalen da cire tallafin mai ya haifar wanda hakan ya jefa mutane cikin matsi, amma suna da fatan hakan zai zamarwa mutanen Nijeriya alheri a gaba.
Wannan dai na zuwa ne daidai lokacin da Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin fara raba hatsi domin ragewar al’umma zafin halin da cire tallafin ya jefa su.
Kazalika, su ma gwamnatocin jihohi a matakansu suna da nasu tsare-tsaren da suke shiryawa wadanda za su yi daidai da bukatar mutanen da suke wakilta.
“Kowace jiha ta tsara abubuwa da yawa da za a yi, yanzu misali mu jihar Jigawa, jiha ce ta manoma don haka tanadinmu na taimaka wa manoma ne.
“Za mu samar musu da abubuwa cikin sauki domin su samu su yi noma cikin sauki, abinci ya wadata, domin samun abinci wadatacce shi ne zai rage halin da ake ciki a yanzu.
“Na farko dai mun karya farashin taki daga 26,000 zuwa 16,000, kuma mun dauki matakai masu tsauri kan cewa sai manomi na kasa ne aka amince a sayarwa da takin,” in ji Namadi.