Gwamnan Jihar Inugu, Mista Peter Mbah, ya ce gwamnatin jihar sa ta samu damar aiwatar da manyan ayyukan raya ƙasa sakamakon cire tallafin mai da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar.
Gwamnan ya faɗi hakan ne a fadar Gwamnatin Jihar Inugu, lokacin da ya karɓi baƙuncin Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, tare da tawagar sa a ziyarar ban-girma da suka kai masa.
- NPA Ta Fito Da Sabuwar Doka Kan Kayan Da Ake Ajiyewa A Tashoshinta
- Bayan Gargadi Daga Gwamnatin Tarayya: Jihohin Arewa 15 Sun Fara Daukar Matakan Dakile Ambaliyar Ruwa
Tawagar ta je jihar ne domin shirin taron tattaunawa tsakanin jami’an Gwamnatin Tarayya da ‘yan ƙasa na tsawon kwanaki biyu a yankin Kudu-maso-gabas.
Ya ce: “A Inugu, mun sami damar cika duk abin da muka yi wa mutanen mu alƙawari a lokacin kamfen, godiya ga jarumtar da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi, wadda ta samar mana da albarkatun da ake buƙata don aiwatar da manyan ayyuka.”
Ya kuma bayyana ayyukan da ake yi a halin yanzu a jihar, waɗanda suka haɗa da gina ajujuwa 7,000, samar gadajen asibiti 3,300, da samar da gonakin gwamnati hekta 2,000 a cikin gundumomi 260 na jihar.
Gwamna Mbah ya yi alƙawarin ci gaba da mara wa manufofin Gwamnatin Tarayya baya, yana mai cewa suna da amfani ga al’ummar jihar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp