Mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, NSA Malam Nuhu Ribadu ya bayyana cewa, cire tallafin man fetur da shugaban kasa Bola Tinubu ya yi ya kawo karshen fasa-kwaurin man fetur da ake yi a fadin kasar nan.
Ribadu ya bayyana haka ne a Abuja ranar Laraba a taron da ake yi na Kwanturola Janar na Hukumar Kwastam, inda ya kara da cewa Nijeriya na tallafawa kasashe makwabta ne kadai saboda fasakwaurin da ake yi a kan iyakokin kasar.
- Salon Zamanantarwa Irin Na Kasar Sin Riba Ce Ga Duniya Baki Daya
- Babban Jami’in Sin Ya Halarci Taron Kolin Shugabannin Kasa Da Kasa Kan Daukar Matakan Daidaita Sauyin Yanayi
“Ni dan yankin kan iyaka ne kuma a kullum ina yawan samun kiraye-kirayen yadda Hukumar Kwastam ke matsa wa masu fasa-kwauri. Amma abin mamaki mutanen da ke taimaka musu sun hada da sojoji amma yanzu komai ya zama tarihi domin duk wadannan janar-janar da jami’an tsaron da ke ba da damar fasa-kwaurin man fetur an kwashe su an maye gurbinsu da wata sabuwar tawaga.”
NSA ya alakanta dimbin yawan man fetur a kasar nan da tsarin tallafin da suke amfana da shi.
“Nijeriya ce kasa daya tilo a duniya da kowa ya zama dan kasuwan mai saboda tallafin man. Kuna iya kirga kusan gidajen mai guda 100 daga Abuja zuwa Kaduna kadai. Saboda biyan tallafin amma ya kare,” in ji shi.