A cikin wannan hali na matsin tattalin arziki, gwamnatin tarayya na kokarin aiwatar da wasu sauye-sauye a bangaren makamashi, ciki har da cire tallafin wutar lantarki.
Jaridarmu ta LEADERSHIP ta ruwaito cewa Ministan Kudi, Wale Edun, ya sanar da haka bayan wani taron majalisar ministoci kwanan nan, inda ya ce shirin sake fasalin bashi zai kammala cikin ‘yan makonni.
- NDLEA Ta Kama Wani Matashi Dan Shekara 29 Da Kwayoyin Tramadol 7,000 A Kano
- A Karo Na 3 Cikin Wata Guda, Jirgin Ruwa Ya Sake Kifewa A Sakkwato
Shirin ya kuma hada da karin kudin wutar lantarki ga manyan masu amfani, matakan da gwamnatin tarayya ke sa ran za ta samu fiye da Naira 1 tiriliyan a kowace shekara.
A cewar Edun, gwamnati za ta gabatar da tsarin pay-as-you-go ga masu amfani da wutar lantarki domin kawo karshen tallafin gwamnati a wannan bangare.
Sai dai, Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) ta yi watsi da wannan shawara, tana mai cewa hakan zai jefa miliyoyin ma’aikata da iyalansu cikin duhu, wahala, talauci, da kiyayya ga gwamnati.
Upah ya yi gargadi cewa wadannan tasirin ba za su tsaya a gidaje kawai ba, domin al’ummar masu kasuwanci ma za su sha da kyar.
Ya ce: “Kungiyar ‘yan kasuwa za ta fuskanci matsananciyar illa, domin karin kudin wuta ba abu ne mai kyau ga kasuwanci a ko’ina ba. lamarin zai haifar da tsada ta fannin sarrafa kaya, cunkoson kaya da ayyuka, saboda karancin saye, rufe masana’antu da dama, sallamar ma’aikata, tare da barazanar zamantakewa a cikin al’umma,” in ji shi.
Upah ya kara zargin gwamnati da kamfanonin wutar lantarki da yin hadin baki.
Ya ce: “Akwai haramtacciyar alaka tsakaninsu. Wannan yana nuna muku girman lalacewa da rikice-rikicen da ke cikin tsarin,” in ji shi.
Upah ya soki tsarin kebancewar harkar wutar lantarki, yana mai cewa yana bukatar a sake duba shi, ko ma a soke shi gaba daya.
Ya nuna cewa in ban da cin hanci da rashawa da gazawa da babu abin da gwamnati za ta nuna, yana mai cewa rabon kudaden da gwamnati ta yi zuwa yanzu sun fi na lokacin NEPA, amma babu wani ci gaba mai ma’ana a harkar samar da wutar lantarki.
Ya bayyana hujjar cewa babu daya daga cikin tallafin da ya nuna samun ingantacciyar wutar lantarki, yayin da hukumomin bangaren wutar har yanzu suke ikirarin cewa gwamnati tana da bashi, abin da ya haifar da shakku game da kwangilolin da aka sanya hannu da kuma sahihancinsu.
Upah ya yi rantsuwa cewa NLC za ta ci gaba da shiri da kuma daukar mataki ta hanyar hukumomin da suka dace, domin ta ba da amsa yadda ya kamata idan matakan gwamnati na cire tallafi suka tabbata.
“Majalisar ta yi iya kokarinta wajen fadakar da gwamnati da hukumominta masu dacewa kan abin da ya kamata a yi, sannan muka bi shi da zanga-zangar tituna lokacin da ba su yi abin da ya dace ba.
“Duk da haka, Majalisar ba ta da niyyar yin watsi da batun. Hukumomin da suka dace. Majalisar za su hadu su kuma mayar da martani idan gwamnati ta dauki mataki,” in ji Upah.
Kungiyar kwadago ta jawo hankalin gwamnatin tarayya kan rahoton gwamnatin Amurka da ya nuna cewa mafi karancin albashi na Naira 70,000 ba zai wadatar kan fitar da miliyoyin ‘yan kasa daga talauci ba, tana mai kawo misalai da karancin iya aiwatar da tsaro tare da rushewar darajar Naira.
A cikin Rahotannin Kasashen 2024 kan Hanyoyin ‘Yancin Dan Adam, da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fitar a ranar 12 ga Agusta, 2025, an bayyana cewa mafi karancin albashin Nijeriya, wanda darajarsa yanzu ke kusan Dala 47.90 a kowane wata, ya fadi kasa da matakin kudin shiga.
“Dokar Gyaran Mafi Karancin Albashi ta 2024 ta ninka mafi karancin albashi zuwa Naira 70,000 (Dala 47.90) a wata. Duk da karin, faduwar darajar kudi ta sanya mafi karancin albashi bai fi matakin kudin da zai jefa mutane cikin talauci ba,” in ji rahoton.
Rahoton ya kara bayyana cewa aiwatar da dokar albashi a fadin kasar na da rauni, inda ma’aikata da dama ba su cikin wadanda dokar ta shafa.
“Dokar ta tanadi mafi karancin albashi na kasa ga dukkan ma’aikatan gwamnati da masu zaman kansu da ke da ma’aikata guda 25 ko fiye haka, banda ma’aikatan noma da na yanayi, da wadanda ke aiki da kwangila ko kwamitoci, da sauransu.”
“Yawancin masu aiki suna da kasa da ma’aikata 25, don haka mafi yawan ma’aikata ba su shiga cikin wadanda dokar ta shafa ba. Wasu jihohi ma sun ki aiwatar da dokar mafi karancin albashi, suna kiran karancin kudi a matsayin dalili,” in ji gwamnatin Amurka.
Upah ya kara da cewa, har ma gwamnatocin kasashen waje sun san da matsanancin halin talauci a cikin kasar.
Amurka, a cikin rahoton, ta kuma lura cewa ko da yake dokar ta wajabta awanni 40 na aiki a mako, hutun shekara na makonni biyu zuwa hudu, da biyan kudin karin aiki da na hutu, har yanzu akwai gibi wajen fayyace karin albashi da karin lokaci.
“Dokar ta haramta yawan tilasta karin aiki ga ma’aikatan farar hula na gwamnati,” in ji rahoton.
Sai dai rahoton Amurka ya soki karfin gwamnatin Nijeriya wajen aiwatar da ka’idodin aiki.
“Gwamnatin tarayya ba ta cika aiwatar da mafi karancin albashi, biyan karin lokaci, da dokokin tsaron muhalli da lafiya na wuraren aiki (OSH) ba. Hukuncin da ake sanyawa kankani ne kuma ba su yi daidai da sauran laifuka kamar almundahana ba, kuma an samu dadadden lokaci ana iya cewa ba a cika amfani da su ba,” in ji rahoton.
Tinubu ya kamata ya rage wa ‘yan Nijeriya nauyi, ba ya kara musu ba – Secondus, Abdullahi
A nasa bangaren, tsohon shugaban jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na kasa, Prince Uche Secondus, ya roki Shugaban Kasa da ya sake tunani kan shirin cire tallafin wutar lantarki
‘Wannan ba lokacin yin wasa da walwalar ‘yan Nijeriya ba ne. ‘Yan Nijeriya sun dauriya sosai a karkashin wannan gwamnati. Shugaban kasa bai kamata ya kara musu wata azaba ba.
‘‘Maimakon ya kara musu nauyi, ina ganin ya kamata shugaban kasa ya yi tunanin yadda zai rage musu nauyin,’’ in ji shi.
Wani masanin tattalin arziki, Gabriel Adewuyi, ya ce ko da yake tallafi ba shi ne mafi alheri ga gwamnati ba, amma albashin da ma’aikata ke karba yanzu ba zai iya kara raunana kudin shiga ba.
A cewarsa, ‘‘Mun yarda cewa tallafi watakila ba shi da kyau ga tattalin arziki, amma babu wata gwamnati a duniya da ba ta tallafa wa ‘yan kasarta ba.
‘‘Dukkan kasashe masu ci gaba suna tallafa wa tattalin arzikinsu ta hanyoyi daban-daban. Shugaba Bola Tinubu ya kamata ya mai da hankali wajen kara yawan samarwa da kafa masana’antu don talakawa.
‘‘Har ila yau, zabe na 2027 na tafe. Shin wannan shi ne lokacin da ya dace ya kara wa masu zabe radadi? Lokacin da yake yakin neman zabe shekaru uku da suka wuce, ya ce farashin man fetur zai sauka. Shin ya sauka?
‘‘Da zarar ya ci zabe kuma ya hau mulki, abin farko da ya yi shi ne cire tallafi ba tare da ya samar da wani abu da zai rage wa ‘yan Nijeriya tasirin hakan ba. Don Allah, ku taimaka a roke shi ya sassauta.’’
Haka kuma, mai magana da yawun kungiyar adawa, Mallam Bolaji Abdullahi, ya zargi gwamnati da rashin kula da walwalar ‘yan Nijeriya.
Ya ce, ‘‘Ku dubi halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, amma mutanen gwamnati kamar ba su sani ba.
‘‘Shi ya sa suke son kara wa kansu albashi. To ku fada min, Naira 70,000 a kasuwa yanzu ya ishi ga uba mai mata daya da ‘ya’ya uku? Mene ne zai iya yi da wannan kudi?
‘‘Buhun shinkafa ya fi albashin mafi karancin albashi. Yanzu kuma kuna ce wa ma’aikata su daure belt dinsu don kada wandonsu ya fadio saboda rama, amma na jami’an gwamnati na tsinkewa saboda nauyi da annashuwa.
‘‘Walwala da tsaron al’umma su ne manyan ayyukan gwamnati. To ku fada min, shin wannan gwamnati tana samar da su? Duk wannan abin lokaci ne kawai; kwanciyar hankali zai ta zo nan gaba,’’ in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp