Yayin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping ke yi a kasar Rasha, a yau Talata 21 ga wata bisa agogon wurin, babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG a takaice, da gidan talabijin da rediyo na kasar Rasha wato VGTRK a takaice, sun rattaba hannu kan takardar bayani ta hadin gwiwa a birnin Moscow, da nufin tabbatar da yarjejeniyar da shugabannin bangarorin biyu suka cimma, tare da inganta hadin gwiwa daga dukkan fannoni. Kana bangarorin biyu sun amince su habaka, da amfani da bayanan bidiyo na tarihi tare. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp