ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, June 22, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Gwamna Abba Ya Yi Alhinin Rasuwar Muhammadu Buhari

by Abubakar Sulaiman
11 months ago
Abba

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Sowore A Gidan Yarin Kuje

Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana alhini bisa rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, yana mai cewa marigayin ya kasance mutum mai ɗa’a, da kishin ƙasa da ƙoƙarin ganin ci gaban Nijeriya.

A cikin sakon ta’aziyya da ya fitar ranar 13 ga Yuli, 2025, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa Buhari ya yi rayuwa ta sadaukarwa tun lokacin mulkinsa na Soja har zuwa zama shugaban ƙasa da aka zaɓa ta dimokuraɗiyya. Ya ce Buhari ya kasance gwarzo da ya tsaya tsayin daka wajen zaman lafiya da ɗorewar haɗin kan ƙasa.

  • Mutuwar Buhari Babban Rashi Ne Ga Nijeriya – Kashim Shettima
  • Ina Cike Da Alhinin Rasuwar Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari — Atiku

“Shugaba Muhammadu Buhari ya sadaukar da rayuwarsa gaba ɗaya wajen yi wa ƙasa hidima da gaskiya da riƙon amana. Sauƙin rayuwarsa da jajircewarsa wajen kare talakawa, abubuwa ne da za su ci gaba da kasancewa abin koyi,” in ji Gwamna Yusuf.

ADVERTISEMENT

Gwamnan ya mika saƙon ta’aziyya ga iyalan marigayin, da gwamnatin Jihar Katsina, da ɗaukacin al’ummar Nijeriya. Ya kuma roƙi Allah Ya gafarta masa, Ya karɓi rayuwarsa cikin rahama, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, da kuma bai wa ‘yan Nijeriya ƙarfin zuciya wajen jure wannan babban rashi.

Abba
Abubakar Sulaiman
Website |  + postsBio
  • Abubakar Sulaiman
    Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Sowore A Gidan Yarin Kuje
  • Abubakar Sulaiman
    Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato
  • Abubakar Sulaiman
    Yanzu-Yanzu: Firaiministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus
  • Abubakar Sulaiman
    Sojoji Sun Ceto Mutanen Da Aka Sace, Sun Daƙile Hari A Kaduna Da Zamfara

MASU ALAKA

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Sowore A Gidan Yarin Kuje
Labarai

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Tsare Sowore A Gidan Yarin Kuje

June 22, 2026
Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato
Manyan Labarai

Yanzu-Yanzu: An Kashe Manoma 18 Da Raunata Wasu A Wani Sabon Hari A Filato

June 22, 2026
Yanzu-Yanzu: Firaiministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus
Labarai

Yanzu-Yanzu: Firaiministan Birtaniya Keir Starmer Ya Yi Murabus

June 22, 2026
Next Post
Za A Yi Taron Shugabannin Matasa Na Farko Na Dandalin Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka A Nanjing

Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna

Fisatattun Matasa Sun Ƙone Wata Mata Ƙurmus Kan Jita-Jitar Satar Yara A Kaduna

June 22, 2026

Mutane 842 Ne Suka Rasa Ransu, Aka Yi Garkuwa Da Sama Da 270 A Watan Mayu – Rahoto

June 21, 2026
PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar  Jamiyyar

PRP Ta Zargi Kwankwaso Da Saye Fom Ɗin Takarar Jamiyyar

June 21, 2026
An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

An Ƙaddamar Da Dakarun Tsaron Daji 2,187 A Bauchi

June 21, 2026
An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

An Sanar Da Wadanda Suka Lashe Golden Goblet Na Bikin Fina-Finen Kasa Da Kasa Na Shanghai Karo Na 28

June 21, 2026
Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

Cibiyar CBA Ta Kenya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Wata Cibiyar Sin Wajen Bunkasa Noma Da Cinikayyar Lemar Kwadi

June 21, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.