A yau 11 ga wata a birnin Hanoi, gabannin ziyarar aiki ta babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping a Vietnam, an kaddamar da fina-finai da shirye-shiryen talabijin na kasar Sin masu inganci da rukunin gidajen radiyo da talabijin na kasar Sin CMG ya shirya. Za a kuma watsa ayyuka takwas da CMG ya shirya a muhimman kafafen yada labaru na Vietnam, wadanda suka nuna nasarorin da aka samu na zamantar da kasar Sin da kuma shahararrun al’adun gargajiya na Sinawa daga mabambantan mahanga. (Mohammed Yahaya)