A jiya ne babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya lashe lambobin yabo guda 4, yayin wani biki da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, ya shirya don bayar da lambar yabo na ingancin ayyukan watsa labaru na Olympics a sassa 9, bisa gudummawar da suka bayar a lokacin gasar wasannin Olympics ta Beijing 2022.
Babban rukunin CMG, ya lashe lambar zinare, a matsayin wanda ke kan gaba wajen watsa shirin Olympics mafi kyau da kuma kyawun aiki mai dorewa, sai kuma lambar azurfa da ya lashe saboda mafi kyawun kirkire-kirkire da tsari da rashin katsewar shirye-shiryen da yake watsawa
Shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasa da kasa, Thomas Bach, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, wadannan lambobin yabo, sun yi na’am da irin basira, da sha’awa da kirkire-kirkire da masu hakkin yada labarai ke nunawa yayin da suke raba bayanai masu nishadantarwa na wasannin Olympic ga masu kallo da sauraronsu. (Ibrahim)