Gabanin bude taron hadin gwiwar kasa da kasa na shawarar Ziri Daya da Hanya Daya wato BRF karo na uku a gobe Talata, babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya gudanar da biki a jajiberin bude taron, na nuna fina-finan “documentary”, ta yaruwa daban daban a nan birnin Beijing, bisa jigon “Kama hanyar samar da wadata”.
Cikin jawabin sa yayin kaddamar da fina-finan, shugaban CMG Shen Haixiong, ya ce tarihin hanyar siliki, da na kasar Sin, dukkanin su suna gudana cikin kyakkyawan yanayi, kuma mafarkin cimma nasarar su zai zama gaskiya a zukatun al’ummun duniya baki daya. Ya ce kawance hanya ce ta rungumar juna, kuma kaunar juna yare ne na dukkanin bil adama. Don haka a duniyar yau, dukkanin sassa na ci gaba da dunkulewa.
Shen Haixiong ya kara da cewa, kafar CMG za ta ci gaba da haska fitilar wayewar kai ta hanyar kirkire-kirkire, tare da baiwa duniya damar jin duriyar bunkasar kasar Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)