Kamfanin gungun gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, zai watsa bikin bude zama na 3 na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, wato CPPCC karo na 14 a gobe Talata 4 ga watan nan.
Za a bude taron ne da karfe 3 na rana bisa agogon Beijing. Kuma shugaban majalisar ta CPPCC Wang Huning, zai mika rahoton aikin zaunannen kwamitin koli na majalissar CPPCC.
Kazalika a yayin zaman, kafofin rediyo da na talabijin daban daban dake karkashin CMG, za su gudanar da shirye-shirye kai tsaye, kana su ma sabbin kafofin sadarwa na zamani za su shiga a dama da su a wannan aiki. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp